Iya Kokarinka, Iya Albashinka: Gwamnatin Tarayya Za Ta Kawo Sabon Tsarin Biyan Ma’aikata

Iya Kokarinka, Iya Albashinka: Gwamnatin Tarayya Za Ta Kawo Sabon Tsarin Biyan Ma’aikata

  • Gwamnatin tarayya ta ce tana kan duba yiwuwar fara amfani da wani sabon tsarin biyan albashi ga ma’aikatan gwamnati
  • Shugaban hukumar samar da ingantaccen aiki ta kasa, Nasir Raji-Mustapha ya ce za a rika biyan ma'aikata gwargadon kokarinsu
  • Raji-Mustapha ya bayana cewa da tsarin 'iya aikinka, iya albashinka', ma'aikata a mataki daya na iya samun albashi daban-daban

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - A jiya Litinin, Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa tana kan nazarin yiwuwar fara amfani da wani sabon tsarin biyan albashi ga ma’aikatan gwamnati.

Gwamnati ta ce idan aka fara amfani da sabon tsarin, ma’aikatan da ke a mataki daya za su iya samun albashi daban-daban, jaridar The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta hada kai da Enugu domin sarrafa rogo zuwa sinadarin fetur

Gwamnati na duba yiwuwar bullo da sabon tsarin albashin ma'aikata
Gwamnatin tarayya na nazarin amfani da kokarin ma'aikata wajen biyansu albashi. Hoto: Deborah Tolu-Kolawole
Asali: UGC

Gwamnatin ta ce za ta fara amfani da tsarin 'iya aikinka, iya albashinka' ne saboda ta fahimci cewa 'yin aiki tukuru kuma mai inganci' shi ne babban abin da ke kawo ci gaban tattalin arzikin kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnati na nazarin sabon tsarin albashi

Shugaban hukumar samar da ingantaccen aiki ta kasa, Nasir Raji-Mustapha ne ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin ganawa da manema labarai na kungiyar kwadago.

Nasir Raji-Mustapha ya ce:

“Muna shirin samar da tsarin biyan albashi gwargadon kokarin ma'akaci wanda zai tabbatar da cewa wadanda suka yi aiki tukuru sun samu ladan kokarinsu.
"Haka zalika, wannan tsarin ba zai yi la’akari da matakin aiki ba, kenan, ma'aikata a mataki daya na iya samun albashi daban-daban."

Albashi: "Za a mika rahoto" - Raji-Mustapha

Jaridar The Guardian ta ruwaito shugaban hukumar NPC ya jaddada cewa:

Kara karanta wannan

Rayuwa za ta yi sauki kuma abinci zai wadata a mulkina, Tinubu ya dauki alkawari

"Mun tuntubi kungiyoyin kwadago saboda suna a matsayin masu ruwa da tsaki na musamman a tsarin. Abin farin ciki shi ne sun ba mu tabbacin goyon bayansu.

Ya kara da cewa rahoton farko na binciken tsarin ya kammala, amma za su kara tuntubar masu ruwa da tsaki domin bayar da shawarwari kafin gabatar da shi ga gwamnati.

Gwamnati za ta sayo motocin CNG

A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaba Bola Tinubu ya ba da umarnin sayo motocin da ke amfani da gas din CNG domin rage kashe kudi kan man fetur.

A yayin taron majalisar zartarwar tarayya a jiya Litinin, Tinubu ya umarci hukumomi da ma'aikatu da sauya dukkanin motoci da janareta da suke amfani da su daga fetur zuwa CNG.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.