Sha'awa na damunmu, muna bukatar maza don kwanciya - Matan gidan yari

Sha'awa na damunmu, muna bukatar maza don kwanciya - Matan gidan yari

  • Sau da yawa mutum baya sanin amfanin ‘yancin shi har sai ya kubuce mishi
  • Wasu mata masu matukar bukatar jima’i da ke gidan yarin Malindi Kilifi a kasar Kenya sun roki gwamnatin kasar
  • Matan sun bayyana a matse ne kuma cikin takura yayin da suka bayyana wannan bukatar ga gwamnatin kasar

Wasu mata masu matukar bukatar jima’i da ke gidan yarin Malindi Kilifi a kasar Kenya sun roki gwamnatin kasar da ta saka sabuwar doka da za ta bar su jin dadin junansu da mazansu yayin da suka kai musu ziyara, jaridar pulse.ng ta ruwaito.

Matan sun bayyana a matse ne kuma cikin takura yayin da suka bayyana wannan bukatar ga gwamnatin kasar.

Daya daga cikin ‘yan gidan yarin, Sofia Swaleh, wacce ke fuskantar hukuncin daurin rai da rai tayi magana a madadin ‘yan uwanta mata na gidan.

Kara karanta wannan

Mahara Sun Banka Wa Gidaje 10 Wuta A Wani Unguwa A Kano

Kamar yadda ta ce, lokacin da ake ba mazansu na ganinsu yayin da aka kawo musu ziyara yayi kadan. Hakazalika basu samun damar kwanciya da mazansu din.

Sha'awa na damunmu, muna bukatar maza don kwanciya - Matan gidan yari
Sha'awa na damunmu, muna bukatar maza don kwanciya - Matan gidan yari
Asali: Depositphotos

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

KU KARANTA: Dan uwa ya kashe dan uwan shi a kan Aku guda biyu

Gwamnati ta hannun shugabannin gidan gyaran halin ya kamata su kirkiro dokar da za ta bar matan da ke gidan yarin samun damar kwanciya da mazansu na aure bayan sun kawo musu ziyara,” Swaleh tace.

A halin yanzu, matukar aka yankewa mutum hukunci na zaman gidan gyaran hali, da yawa daga cikin hakkokinsa na dan kasa kan bi ruwa.

Rahotanni sun bayyana cewa an samu irin wannan korafin a 2014 amma gwamnatin kasar tayi watsi dasu tare da cewa bata shirya musu ba.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC Tayi Nasarar Daure 'Yan Damfara 2, 800 a Watanni 10 a 2022

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel