Kwamishina Ya Umurci 'Yan Sanda da ’Yan Banga Su Ceto Ma’aikatan Dangote a Edo

Kwamishina Ya Umurci 'Yan Sanda da ’Yan Banga Su Ceto Ma’aikatan Dangote a Edo

  • Kwamishinan yan sandan jihar Edo, CP Funsho Adegboyo ya bada umurnin ceto ma'aikatan kamfanin Dangote da aka sace
  • Kwamishinan ya bada umurnin ne yayin da ya kai ziyarar jaje kamfanin simintin Dangote da ke jihar Edo
  • CP Funsho Adegboyo ya kuma bayyana halin da wadanda aka raunata yayin harin ke ciki a asibitin Halimatu Musa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Edo - Kwamishinan yan sandan jihar Edo, Funsho Adegboyo ya ba jami'ansa umurnin ceto ma'aikatan kamfanin Dangote da aka sace cikin gaggawa.

Police Ng
An yi hadaka tsakanin 'yan sanda da 'yan banga kan ceto ma'aikatan Dangote a jihar Edo. Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Facebook

Kwamishinan ya ba da umurnin ne ga shugaban ƴan sandan yankin Okpella da ke karamar hukumar Etsako.

Kara karanta wannan

Mutanen Arewa sun taso Ministan Tinubu a gaba sai ya yi murabus daga kujerarsa

Rahoton jaridar Leadership ya nuna cewa kwamishinan ya umurci jami'an rundunarsa da su yi haɗaka da ƴan farauta da yan banga wurin gudanar da aikin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaushe aka sace ma'aikatan Dangote a Edo?

A ranar Litinin da ta gabata ne masu garkuwa da mutane suka sace ma'aikatan kamfanin simintin Dangote a jiha Edo.

Rundunar ƴan sandan ta tabbatar da cewa an kama ma'aikatan ne yayin da suke dawowa daga aiki da yamma.

Jawabin kakakin yan sandan jihar Edo

Kakakin rundunar yan sandan jihar, Chidi Nwabuzor ya ce sun samu duba wadanda suka ji raunuka yayin harin a asibiti kuma suna samun sauki.

Kakakin ya tabbatar da cewa sun samu kiran gaggawa a lokacin da aka tare motar ma'aikatan a ranar Litinin, rahoton Channels Television.

Amma kafin zuwan jami'ansu bata garin da ake zargi masu garkuwa da mutane ne sun dauke wasu daga cikin ma'aikatan sun shiga daji da su.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai mummunan hari yayin da suka sace ma'aikatan kamfanin Dangote

Saboda haka ne kwamishinan yan sandan jihar ya yi umurni ga yan sandan da ke yankin su yi haɗaka wurin ceto su cikin gaggawa.

Kwamishinan ya bada umurnin ne yayin da ya kai ziyara kamfanin simintin Dangote da ke jihar ta Edo.

Gwamnati za ta gana da kamfanonin siminti

A wani rahoton, kun ji cewa yayin da ake fama da tsadar kaya musamman bangaren siminti, Gwamnatin Tarayya ta kira ganawa ta musamman.

Ministan Ayyuka, Dave Umahi shi ne ya bukaci ganawar da masu sarrafa siminti a kasar kamar Dangote da BUA da kuma Lafarge domin duba yiwuwar sauke farashi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel