'Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari Yayin da Suka Sace Ma'aikatan Kamfanin Dangote

'Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari Yayin da Suka Sace Ma'aikatan Kamfanin Dangote

  • An shiga fargaba bayan wasu 'yan bindiga sun farmaki ma'aikatan kamfanin simintin Dangote da ke jihar Edo
  • Maharan sun kai hari kan ma'aikatan a yankin Okpella da ke jihar inda suka sace da dama daga cikinsu da raunata wasu
  • Kakakin kamfanin da ke yankin Okpella, Michael Odofin ya tabbatar da faruwar lamarin a jiya Litinin 13 ga watan Mayu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Edo - Wasu 'yan bindiga sun sace ma'aikatan kamfanin simintin Dangote da dama a jihar Edo.

Maharan sun kai harin ne tare da jikkata wasu ma'aikata a yankin Okpella da ke kusa da Okene na jihar Kogi.

Kara karanta wannan

An shiga fargaba bayan cafke matashi dauke da bam a Jos yana kokarin tayarwa

Yan bindiga sun kai hari kan ma'aikatan kamfanin Dangote
Yan Bindiga sun yi garkuwa da wasu ma'aikatan kamfanin Dangote. Hoto: Nigeria Police Force.
Asali: Facebook

Yaushe ƴan bindiga suka dauke ma'aikatan Dangote?

Lamarin ya faru ne a jiya Litinin 13 ga watan Mayu lokacin da ma'aikatan ke dawowa daga aiki a kamfanin simintin Dangote, cewar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata majiya ta tabbatarwa Tribune cewa maharan sun farmaki wata motar bas mai dauke da ma'aikatan kamfanin.

"Mutane da dama sun raunata, wasu na cikin daji, wani abokina ya gamu da tsautsayi an harbe shi da harsashi."
"Maharan sun farmaki wata motar bas dauke da ma'aikata a yankin Okpella da ke jihar Edo."

- Majiyar

Kamfanin Dangote ya yi martani kan harin

Kakakin kamfanin simintin da ke Okpella, Michael Odofin ya tabbatar da faruwar lamarin a jiya Litinin 13 ga watan Mayu.

Sai dai bai ba da cikakken bayani game da harin ba inda ya ce babu wanda ya rasa ransa sakamakon farmakin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga: Aliero sun tafka barna, sun hallaka sojoji, jikkata wasu 11 a Katsina

Miyagu a kwanakin nan sun addabi jihar Kogi inda suke kai hare-hare tare yin ajalin mutane ba ƙaƙƙautawa.

Sojojin sun hallaka kasurguman 'yan bindiga

A wani labarin, an ji dakarun sojoji sun yi ajalin wasu kasurguman 'yan bindiga a jihar Kaduna bayan wani farmaki da suka kai.

Sojojin sun hallaka 'yan bindiga hudu ciki har da hatsabibin ɗan ta'adda, Dogo Bangaje da wasu miyagu guda uku.

Kwamishinan tsaron cikin gida a Kaduna, Samuel Aruwan shi ya tabbatar da haka inda ya ce farmakin ya faru ne a karamar hukumar Giwa da ke jihar bayan samun bayanai sirri.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.