'Yan bindiga: ‘Rashin Tsaro a Arewa Zai Haifar da Babbar Fitina a Yammacin Afrika’, Gwamna

'Yan bindiga: ‘Rashin Tsaro a Arewa Zai Haifar da Babbar Fitina a Yammacin Afrika’, Gwamna

  • Gwamnan jihar Gombe, Alhaji Inuwa Yahaya ya koka kan yadda matsalar tsaro ke cigaba da zama barazana ga Arewa
  • Gwamna Inuwa Yahaya ya magantu ne yau a jihar Gombe yayin da matan gwamnonin Arewa suka kai masa ziyarar ban girma
  • Ya kuma ambaci sauran matsalolin da suka addabi yankin Arewa tare da bayyana hanyoyin da za a shawo kansu cikin sauki

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe - Gwamnan jihar Gombe, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya ya koka kan yadda matsalar tsaro ta ki karewa a Arewacin Najeriya.

Gombe governor
Gwamnan Gombe ya ce dole a kara kokari kan magance matsalar tsaro. Hoto: Isma'il Uba Misilli
Asali: Facebook

Gwamnan wanda shi ne shugaban gwamnonin Arewa ya yi jawabin ne a yau Talata yayin ganawa da ya yi da matan gwamnonin Arewa Gombe.

Kara karanta wannan

Rivers: Gwamnan PDP ya ɗauki zafi, ya sha alwashin bincikar Ministan Bola Tinubu

Jawabin gwamna Inuwa kan tsaro

A bayanan da mai taimaka masa a harkokin sadarwa, Isma'ila Uba Misilli ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya nuna cewa dole a tashi tsaye wurin magance matsalar tsaro a Arewa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar gwamnan, idan matsalar ta cigaba za ta shafi dukkan yankunan Najeriya da kuma haifar da rikici babba a yammacin Afirka.

Yadda shan kwaya ke zama barazanan Arewa

A bangaren shan kwaya kuwa, gwamnan ya ce shaye-shaye na cikin abubuwan da suke kara karfafa matsalolin yan bindiga a Arewa.

Saboda haka ya yi kira ga gwamnoni da masu ruwa da tsaki kan dagewa wurin neman mafita kan matsalar shaye-shaye.

Jawabin gwamna Inuwa a kan Ilimi

Har ila yau gwamnan ya zanta kan matsalar samar da ilimi ingantacce da ta addabi Arewacin Najeriya

Ya ce rashin ilimi ingantacce yana daga cikin abubuwan da suka hana yankin cigaba yadda ya kamata.

Kara karanta wannan

A karshe, Tsohon Gwamna Yahaya Bello Zai Gurfana a Gaban Babbar Kotu a Abuja

Gwamna Inuwa ya kuma koka kan yadda yaran da ba su zuwa makaranta suka yawaita a Arewacin Najeriya.

A cewarsa, dole a hada karfi da karfe wurin ganin an magance matsalolin domin tabbatar da cigaban yankin.

Hanyar samun mafita ga Arewa

A karshe gwaman ya yi kira kan samun hadin kai tsakanin kungiyar matan gwamnonin Arewa da kungiyar gwamnoni domin magance matsalolin yankin.

Saboda a cewarsa matan gwamnonin za su bada gudunmawa sosai musamman wajen magance matsalolin mata.

Yan bindiga sun kai hari Kaduna

A rahoton, kun ji cewa yan bindiga sun raba mutane sama da 200,000 da muhallansu a yankunan kananan hukumomi 12 na jihar Kaduna.

Gwamnatin Kaduna karkashin Malam Uba Sani ta ce mutane 289,375 ne suka gudu suka bar gida a garuruwa 551 saboda matsalar tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng