Katsina: "Yadda 'Yan Bindiga Suka Shirya Tuggu, Suka Kashe Sojoji" Inji DHQ

Katsina: "Yadda 'Yan Bindiga Suka Shirya Tuggu, Suka Kashe Sojoji" Inji DHQ

  • Rundunar sojojin Najeriya ta tabbatar da mutuwar jami’anta guda 4 a harin da ‘yan ta’adda su ka kai jihar Katsina, yayin da aka jikkata wadansu a Zamfara
  • Daraktan tsaro kan yada labaran rundunar ta kasa, Manjo Janaral Edward Buba ya tabbatar da cewa 'yan daba sun kai hari sansanin sojoji da ke karamar hukumar Faskari
  • A cewarsa a wani harin kwantan bauna daban da aka kaiwa jami'ansu da ke aiki a jihar Zamfara, wasu sojoji biyar sun jikkata yayin da suka fatattaki bata-garin

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Katsina-Rundunar sojojin Najeriya ta tabbatar da kisan wasu jami’anta da ke aiki da ‘operation hadarin daji’ guda hudu a jihar Katsina.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari Benue, sun halaka mace mai juna 2 da wasu mutane 10

Rahotanni sun bayyana cewa wasu ‘yan ta’adda sun kai hari sansanin sojoji a karamar hukumar faskari da ke jihar Katsina ranar Lahadi.

Rundunar sojojin Najeriya
Sojoji 4 sun rasu a harin Katsina(An yi amfani da hoton nan domin misali) Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Darektan yada labarai a hedkwatar tsaro, Edward Buba, ya tabbatarwa Daily Trust cewa mutum hudu ne su ke da tabbacin sun rasu ba biyar ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Manjo Janar Edward Buba ya bayyana cewa an kai harin kwantan bauna kan jami’ai biyar da ke tsaron iyakar Najeriya.

An kara kai hari kan sojoji

A rahoton da rundunar sojojin kasar nan ta fitar dauke da sa hannun Manjo Janaral Edward Buba ya bayyana cewa wasu ‘yan ta’adda sun kai hari kan wasu jami’an ta a a jihar Zamfara.

Ya ce harin da aka kai ya yi sanadiyyar mutuwar jami’anta guda hudu a kauyen Kuran Mota dake titin Alikere Yarmalimai a jihar Zamfara, kamar yadda The Guardian ta wallafa.

Kara karanta wannan

Jami'an DSS sun kai samame harabar kotu ana cikin shari'a, sun kama mutum 2

Manjo Janar Edward Buba ya ce duk da rundunar ta samu asarar rayuka da jikkatar wadansu, amma sojojin sun yi galaba a kan ‘yan ta’addar.

Rundunar ta bayyana cewa babu wani aiki da jami’an sojojin ke fita ba tare da samun galaba a kan wasu ‘yan bindiga ba.

Sojoji sun yi nasara kan 'yan ta'adda

A baya mun ruwaito mu ku cewa jami'an sojojin Najeriya sun samu nasarar ceto wasu mutum biyu yayin da suka fatattaki 'yan bindiga a jihar Katsina.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an kama wani kasungurmin dan ta'adda guda daya, sannan an gano babur guda daya da kuma tarin makamai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel