Yadda Wani Mutum Ya Makance Bayan Ya Auri Makauniya Da Mijinta Ya Tsere Ya Bar Ta, Sun Bada Labarin Soyayyarsu

Yadda Wani Mutum Ya Makance Bayan Ya Auri Makauniya Da Mijinta Ya Tsere Ya Bar Ta, Sun Bada Labarin Soyayyarsu

  • Rashidi Apahamanyi Musasigye ya kamu da soyayyar Lilian wani rana da yayin da ya ke aikinsa
  • Lilian ta yi bayanin cewa tsohon mijinta ya rabu da ita tare da yaya biyu kuma ba ta cancanci soyayyarsa ba
  • Mutumin dan kasar Tanzania, Rashidi ya dage kan bakansa, duk da kallubale, ya auri makauniyar matar

Tanzania - Dangin wani mutum sun rika masa dariya bayan ya kamu da soyayyar wata mata makauniya.

Mutumin mazaunin garin Arusha, a Tanzania, yana wurin aiki ne a lokacin da ya hadu da sabiharsa, duk da cewa ba ta gani da idanunta.

Ma'aurata Makafi
Wani Mutum Ya Makance Bayan Ya Auri Makauniya Da Mijinta Ya Tsere Ya Barta, Sun Bayyana Labarin Soyayyarsu. Hoto: Afrimax
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mutumin dan kasar Tanzania ya shirya auren makauniya

Rashidi Apahamanyi Musasigye ya bayyana soyayyarsa da niyarsa na auren kyakyawan Lilian.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Peter Obi Ya Ce Ko Ƴaƴan Cikinsa Ba Su Yarda Da Shi Idan Ya Yi Alƙawari, Mutane Sun Yi Martani

Lilian ta yi mamakin yadda mutum mai idanunsa lafiya wanda bai taba makanta ba ya zabi a aure ta matsayin matarsa, kamar yadda Arimax English ta bayyana.

Lilian ta bawa Rashidi labarinta mai sosa zuciya, na yadda mijinta ya yi watsi da ita bayan sun haifi yara biyu.

Hakan bai canja niyyar da Rashidi ya yi ba domin ya fada mata yana sonta kuma yana fatan su kasance tare har karshen rayuwarsu.

Mutumin dan Tanzania ya dora wa yan uwansa laifi

Yan uwan Rashidi sun rika masa dariya, suna cewa yana bukatar wani ya taimake shi, ba shi ya taimake ta ba.

Duk da matsaloli daga yan uwansa da kuma cewa Lilian bata taba ganin masoyinta ba, sun yi aure sun fara zama tare.

Amma, bayan yan shekaru kadan, Rashidi, wanda ake kusa kashewa, ya tsinci kansa a gidan yari ba tare da dalili ba, kuma ya makance

Kara karanta wannan

Magidanci Ya Gano Cewa Matarsa Tayi Auren Sirri da Wani Maigadi Duk da Suna da ‘Ya’ya 2

Ya dora laifin faruwar lamarin mara dadi kan yan uwansa, ya yi ikirarin cewa dama ba su taba fatan ganin ya yi nasara a rayuwa ba.

Ma'auratan yan Tanzania ne kokarin sabawa da canje-canje a sabon rayuwarsu

Lilian, wacce ita ma da ta makanta aka haife ta ba, tana tare da shi tana tallafa masa ya koya sabon rayuwa, tana taimaka masa a duk hanyar da za ta iya.

Daga bisani sun haifi da wanda ke gani kuma yana taimaka musu wurin ayyuka da ke bukatar gani.

Rashidi, wanda ya rasa iya amfani da sassan jikinsa na tsawon shekara daya da rabi kafin haduwa da matarsa, yana koyon sabawa da sabuwar rayuwarsu.

Ma'auratan makafi suna bukatar kudi don abinci, biyan kudin haya da kudin makaranta, don dukkansu ba su aiki.

An Haifa Wa Matashin Hadimin Buhari Yarsa Ta Farko, Yan Najeriya Suna Ta Taya Shi Murna

A wani labarin, yan Najeriya sun fara tura sakonnin taya murna ga hadimin Shugaba Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad da matarsa Naeemag, bisa haihuwar yarsu.

Kara karanta wannan

Ta Rabu Da shi Saboda Tayi Sabon Saurayi: Magidanci Ya Ruguza Gidajen Da Ya Ginawa Matarsa Da Surukarsa

Ahmad, ya sanar a shafinsa na Twitter a ranar Juma'a, 16 ga watan Satumba, cewa an haifa masa ya mace, da ya rada wa suna Fatima Bashir Ahmad.

Asali: Legit.ng

Online view pixel