An Haifa Wa Matashin Hadimin Buhari Yarsa Ta Farko, Yan Najeriya Suna Ta Taya Shi Murna

An Haifa Wa Matashin Hadimin Buhari Yarsa Ta Farko, Yan Najeriya Suna Ta Taya Shi Murna

  • An fara tura wa hadimin shugaba Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad, sakonnin taya murna bayan matarsa ta haifi ya mace
  • Ahmad ya sanar da haihuwan a shafinsa na sada zumunta a ranar Juma'a, 16 ga watan Satumba
  • Dan siyasan, haifafan jihar Kano ya bayyana murnarsa bisa haifa masa Fatima, kusan shekaru biyu bayan daurin aurensa da Naeemah

Twitter - Yan Najeriya sun fara tura sakonnin taya murna ga hadimin Shugaba Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad da matarsa Naeemag, bisa haihuwar yarsu.

Ahmad, ya sanar a shafinsa na Twitter a ranar Juma'a, 16 ga watan Satumba, cewa an haifa masa ya mace, da ya rada wa suna Fatima Bashir Ahmad.

Bashir Ahmad
An Haifa Wa Matashin Hadimin Buhari Yarsa Ta Farko, Yan Najeriya Suna Ta Taya Shi Murna. @thecableng
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Buhari Ya Ɗauki Muhimmin Mataki Na Kawo Ƙarshen Yajin Aikin ASUU

Menene sunan yar Bashir Ahmad?

Hadimin shugaban kasar ya bayyana murnarsa na zama mahaifi yayin da ya yi addu'ar Allah ya raya masa yarsa.

Kalamansa:

"Alhamdullilah! Allah ya albarkace mu kuma. Fatima Bashir Ahmad ta iso wannan duniyar a ranar Juma'a.
"Allah ya bata ilimi mai yawa kuma ya dora ta kan hanya madaidaiciya da sunnah Annabin mu (SAW). Mun gode Allah!."

Yaushe Bashir ya yi aure?

An haifi Fatima ne saura kwana biyu auren Bashir da Naeemah ya cika shekaru biyu, an daura aurensu ne a Satumban 2020.

A watan Mayu, Ahmad ya yi murabus daga mukaminsa a matsayin hadimin Shugaba Muhammadu Buhari bisa umurnin da shugaban kasa ya bada ga hadiminsa masu son takara su ajiye aiki.

Amma, ya sha kaye ya gaza samun tikitin dan majalisa mai wakiltar Gaya/Ajingi/Albasu karkashin jam'iyyar APC a Kano gabanin zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel