Zaben 2023: Peter Obi Ya Ce Ko Ƴaƴan Cikinsa Ba Su Yarda Da Shi Idan Ya Yi Alƙawari, Mutane Sun Yi Martani

Zaben 2023: Peter Obi Ya Ce Ko Ƴaƴan Cikinsa Ba Su Yarda Da Shi Idan Ya Yi Alƙawari, Mutane Sun Yi Martani

  • Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP a zaben 2023, ya ce ko yayansa suka nadan magansa a rikoda idan ya yi alkawari a gida
  • Wannan kalaman na tsohon gwamnan jihar Anambra ta janyo cece-kuce a dandalin sada zumunta
  • An yi martanin ne saboda an bukaci dan takarar shugaban kasar ya fada wa yan Najeriya shirin da ya ke yi wa kasar game da lantarki amma ya fara magana game da iyalansa

Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, LP, yana shan suka a soshiyal midiya saboda amsar da ya bada kan tambayar da aka masa game da yadda zai farfado da lantarki a Najeriya.

Mai gabatar da shirye-shirye a gidan talabijin na Arise TV ya ce wannan shine dalilin da yasa ya kamata dan takarar LP din ya fitar da manufofinsa ga kasar a rubuce don mutane su gani su yi nazari.

Kara karanta wannan

Yadda Dan Kwallon Najeriya Ya Nutse Bayan Ceto Fasinjojin 5 A Hatsarin Jirgin Ruwa Da Ya Ritsa Da Su

Mr Peter Obi
2023: Peter Obi Ya Ce Ko Yayansa Ba Su Yarda Da Shi Idan Ya Yi Alkawari, Mutane Sun Yi Martani. Hoto: Mr Peter Obi.
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Menene sabon labari game da Peter Obi

Amma Peter Obi ya cigaba da bayani ya bayyana yadda yayansa a gida ba su yarda da shi kuma suka dagewa sai ya nadi kalamansa a rikoda don su tunatar da shi duk lokacin da bukatan hakan ya tashi.

Tsohon gwmanan na jihar Anambra daga bisani ya ce, "akwai tirakto 70,000 a Punjab."

Da ta ke wallafa bidiyon tattaunawar da aka yi da Peter Obi a shafinta na Twitter, Dannie ta ce:

"Ta yaya za a maka tambaya cewa "menene tsarinka kan lantarki"? kuma zai ka fara sumbatu kan yadda yayanka ba su yarda da kai idan ka yi alkawari?
"Daga karshe, ba kunya zai ka kare da cewa "akwai tirakta 70,000 a Punjab"
"Menene hadinsu don Allah????.

Kara karanta wannan

Sule Lamido: An Kira Ni Fasto A Arewa Saboda Goodluck Jonathan

Zaben 2023: Mataimakiyar Kakakin APC Ya Bayyana Jihohin Arewa Da Obi Zai Iya Cin Zabe

Duba da kara karbuwa da Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, LP, ke kara samu, jam'iyyar APC ta yi wani hasashe kan wasu abubuwa da ka iya faruwa a babban zaben 2023.

Mataimakiyar kakakin kungiyar kamfen din shugaban kasa na APC, Hannatu Musawa, wacce ta yi magana da The Punch a ranar Lahadi, 16 ga watan Oktoba ta ce akwai yiwuwar Obi ya samu kuri'un wasu jihohin arewa da kowane dan takara ke bukata don cin zabe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel