Akwai matsala: Ba za mu bari 'yan Najeriya su tafi Ukraine yaki ba, gwamnatin Buhari

Akwai matsala: Ba za mu bari 'yan Najeriya su tafi Ukraine yaki ba, gwamnatin Buhari

  • Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa, sam bata amince 'yan Najeriya su dauki kafa zuwa Ukraine domin taya kasar yaki da Rasha ba
  • Wannan na zuwa ne jim kadan bayan da 'yan Najeriya suka nuna sha'awar tafiya Ukraine domin taya ta fatattakar Rasha
  • Gwamnati ta ce sam ba daidai bane, kuma za ta yi magana da kasar Ukraine kan wannan lamari na 'yan Najeriya

FCT, Abuja - Wani rahoton jaridar Punch ya ce, Gwamnatin Tarayya ta bayyana rashin amincewarta da ci gaba da yi wa ‘yan Najeriya rajistar shiga yakin Ukraine domin tinkarar sojojin Rasha da ke mamaye da kasar.

Idan baku manta ba, sama da ‘yan Najeriya 150 ne suka nuna sha'awar shiga yakin Ukraine, shugaban kasar , Volodymyr Zelensky, ya bukaci 'yan sa kai daga kasashen duniya su shiga yakin domin tinkarar abokiyar hamayyarta; Rasha.

Kara karanta wannan

A tura su Borno: Jami'in tsaro ya nemi a tura matasan da ke son zuwa Ukraine yaki su yaki Boko Haram

Sai dai da take mayar da martani a wata sanarwa a ranar Litinin, kakakin ma’aikatar harkokin wajen tarayya, Francisca Omayuli, ta ce gwamnatin tarayya ba za ta amince da daukar 'yan Najeriya a tura su Ukraine ba.

'Yan Najeriya ba za su je Ukraine ya ki ba
Akwai matsala: Ba za mu bari 'yan Najeriya su taya Ukraine yaki ba, gwamnatin Buhari | Hoto: crossed-flag-pins.com

Ta kuma jaddada cewa gwamnatin tarayya za ta tattauna da ofishin jakadancin Ukraine a Najeriya da sauran hukumomin da abin ya shafa domin dakile shirin tafiya da 'yan Najeriya zuwa Ukraine.

Sai kun biya N560k: Ukraine ga 'yan Najeriyan da ke son taya ta yakar Rasha

A tun farko, ofishin jakadancin Ukraine a Najeriya ya ce 'yan Najeriya da ke son zuwa Ukraine don yakar sojojin Rasha dole ne su amince da biyan dala 1,000 (kwatankwacin N560,000) kowannen saboda a samar musu da tikiti da biza.

Ofishin Jakadancin ya bayyana haka ne a lokacin da ‘yan sa kai daga Najeriya suka yi dandazo a harabarta a Abuja ranar Alhamis domin bayyana shirinsu na shiga Ukraine da Rasha, inji rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Jirgin jigilar yan Najeriya mazauna Ukraine na biyu ya dira birnin tarayya Abuja

Sakatare na biyu a ofishin jakadancin Ukraine a Najeriya, Bohdan Soltys, ya tabbatar da cewa kowane dan Najeriyan da ke son zuwa Ukraine zai biya dala 1,000.

Soltys ya kuma shaida cewa, zai yi wahala ga 'yan sa kai su tafi zuwa Ukraine yanzu tunda an rufe sararin samaniyar kasar saboda yakin da take yi da Rasha.

A tura su Borno: Jami'in tsaro ya nemi a tura matasan da ke son zuwa Ukraine yaki su yaki Boko Haram

A wani labarin, wata hira da jaridar Punch ta yi da tsohon mataimakin Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Adedayo Adeoye, ranar Juma'a ya bayyana yadda za yi amfani da korarrun sojoji su tallafa wajen yakar Boko Haram.

Ya bayyana haka ne a martani ga korarrarun sojojin da suka bayyana shirin yakar Rasha saboda Ukraine, inda yace kamata ya yi a tura su jihohin Borno, Yobe da sauran jihohin Arewa maso Gabashin Najeriya domin yakar ‘yan ta’adda.

Kara karanta wannan

Ku fara da Boko Haram, tsohon shugaban yan sanda ga yan Najeriya da ke son tunkarar sojojin Rasha

Ya ce kamata ya yi gwamnatin Najeriya ta tashi tsaye wajen zaburarwa tare da sake dawo da sojojin da aka kora domin karfafa yakin da ake yi da Boko Haram da sauran kungiyoyin ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel