Ku fara da Boko Haram, tsohon shugaban yan sanda ga yan Najeriya da ke son tunkarar sojojin Rasha

Ku fara da Boko Haram, tsohon shugaban yan sanda ga yan Najeriya da ke son tunkarar sojojin Rasha

  • Mataimakin sufeto janar na yan sanda mai ritaya, Adedayo Adeoye, ya ce yan Najeriya da ke shirin yakar rundunar Rasha na shirin aikata kisan kai ne
  • A cewar Adeoye, sojojin da aka kora kudi kawai suke so, inda ya ce basu san komai game da yankin ba
  • Tsohon jami’in dan sandan ya bukaci gwamnati da ta zaburar da jami’an domin yakar ta’addancin Najeriya maimakon tunkarar sojojin Rasha

Mataimakin sufeto janar na yan sanda mai ritaya, Adedayo Adeoye, ya bayyana cewa ya kamata a tura sojojin da aka kora wadanda suka nuna shirinsu na yakar sojojin Rasha da suka kai mamaya Ukraine zuwa Borno, Yobe da sauran jihohin arewa maso yamma domin yakar yan ta’adda.

Adeoye ya bayyana hakan ne a wata hira ta musamman da ya yi da jaridar The Punch a ranar Juma’a, 4 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Sai kun biya N560k: Ukraine ga 'yan Najeriyan da ke son taya ta yakar Rasha

A cewarsa, ya kamata gwamnatin Najeriya ta tashi tsaye wajen zaburarwa da dawo da sojojin da aka kora domin karfafa yakin da ake yi da Boko Haram da sauran kungiyoyin ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas.

Ku fara da Boko Haram, tsohon shugaban yan sanda ga yan Najeriya da ke son tunkarar sojojin Rasha
Ku fara da Boko Haram, tsohon shugaban yan sanda ga yan Najeriya da ke son tunkarar sojojin Rasha Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Adeoye ya ce shirin mayakan Najeriyan na zuwa Ukraine kisan kai ne saboda ba su fahimci yankin Kyiv ko kuma fasahar yaki a Turai ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da farko mun dai ji cewa kimanin matasa 115 ‘yan Najeriya, a ranar Talata, 1 ga watan Maris, sun nuna sha'awar shiga yakin kasar Ukraine da Rasha.

Sai dai kuma ofishin jakadancin Ukraine a Najeriya ya ce 'yan Najeriya da ke son zuwa Ukraine don yakar sojojin Rasha dole ne su amince da biyan dala 1,000 (kwatankwacin N560,000) kowannen saboda a samar musu da tikiti da biza.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Rukunin farko na yan Najeriya mazauna Ukraine sun iso Abuja

Sakatare na biyu a ofishin jakadancin Ukraine a Najeriya, Bohdan Soltys, ya tabbatar da cewa kowane dan Najeriyan da ke son zuwa Ukraine zai biya dala 1,000.

Da yake zantawa da Punch, tsohon shugaban yan sandan ya ce tsoffin jami’an tsaron da ke shirin yakar rundunar Rasha na hanyar aikata kisan kai ne.

Ya ce:

“Abun da suke kokarin aikatawa kisan kai ne. kamar ace cinnaka ne ke kokarin yaki da giwa; me suka sani game da kasar da Ukraine? Kawai kudi suke so. Ba zan ba kowa shawarar aikata haka ba.”

Ya kara da cewar:

“Ya kamata gwamnatin tarayya ta zaburar da wadannan sojoji da jami’an yan sanda da aka kora. Idan har suna da ra’ayi a kasuwancin tsaron rayuka da kudiya, a bari su tafi arewa maso yamma da arewa maso gabas domin su yaki yan ta’adda da yan fashi. Wadannan yankuna ne da suka sani sosai.

Kara karanta wannan

Mun zo taya ku yakar Rasha: Dandazon 'yan Najeriya sun cika ofishin jakadancin Ukraine

“Ya kamata gwamnati ta karfafa masu gwiwa domin yakar ta’addancin Najeriya maimakon zuwa Ukraine don fuskantar sojojin Rasha.
“Gaba daya, ya kamata gwamnati ta kira dukka sojoji da suka yi ritaya da wadanda aka kora da ke da ra’ayin dawowa rundunar soji domin yaki da ta’addanci a arewa maso gabas da arewa maso yamma. Ya kamata gwamnati ta zaburar da su, ta basu albashi mai kyau, sannan ta sanya su a karkashin inshora koda wani abu ya faru da su, iyalansu na da bangon jingina.”

Mun zo taya ku yakar Rasha: Dandazon 'yan Najeriya sun cika ofishin jakadancin Ukraine

A baya mun kawo cewa kimanin matasa 115 ‘yan Najeriya ne, a ranar Talata, 1 ga watan Maris, suka nuna sha'awar shiga yakin kasar Ukraine da Rasha.

Matasan da suka yiwa ofishin jakadancin Ukraine da ke Abuja babban birnin Najeriya kawanya, sun kuma sanya sunayensu a cikin wata rajista da ofishin jakadancin ya bayar.

Kara karanta wannan

2023: Dattawan Arewa Sunyi Taro, Sun Yanke Shawarar Goyon Bayan Igbo Ya Maye Gurbin Buhari

Asali: Legit.ng

Online view pixel