A tura su Borno: Jami'in tsaro ya nemi a tura matasan da ke son zuwa Ukraine yaki su yaki Boko Haram

A tura su Borno: Jami'in tsaro ya nemi a tura matasan da ke son zuwa Ukraine yaki su yaki Boko Haram

  • Wani tsohon jami'in dan sanda ya bayyana yadda ya kamata 'yan Najeriya su yi wajen yakar Boko Haram
  • Ya ce maimakon tafiya Ukraine su taya wata kasa yaki, me zai hana su shiga daji domin yakar 'yan ta'adda a Najeriya
  • Wannan na zuwa ne jim kadan bayan da 'yan Najeriya da dama suka nuna sha'awar barin Najeriya suka Ukraine domin taya su yakar Rasha

Najeriya - Wata hira da jaridar Punch ta yi da tsohon mataimakin Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Adedayo Adeoye, ranar Juma'a ya bayyana yadda za yi amfani da korarrun sojoji su tallafa wajen yakar Boko Haram.

Ya bayyana haka ne a martani ga korarrarun sojojin da suka bayyana shirin yakar Rasha saboda Ukraine, inda yace kamata ya yi a tura su jihohin Borno, Yobe da sauran jihohin Arewa maso Gabashin Najeriya domin yakar ‘yan ta’adda.

Kara karanta wannan

Ku fara da Boko Haram, tsohon shugaban yan sanda ga yan Najeriya da ke son tunkarar sojojin Rasha

Yakin Rasha da Ukraine: 'Yan Najeriya sun nuna sha'awar kawo tallafi
Ku yaki Boko Haram tukuna, ba kasar Rasha ba, tsohon jami'in tsaro ga 'yan Najeriya | Hoto: sawahpress.com
Asali: UGC

Ya ce kamata ya yi gwamnatin Najeriya ta tashi tsaye wajen zaburarwa tare da sake dawo da sojojin da aka kora domin karfafa yakin da ake yi da Boko Haram da sauran kungiyoyin ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas.

Adeoye ya ce shirin da 'yan Najeriya ke yi na kaiwa kasar Ukraine domin fuskantar Rasha shirin kashe kai ne kuma basu fahimci irin hadarin da hakan ke tattare dashi ba.

Muna neman a taya mu yakar Rasha - Ukraine

Idan baku manta ba, mun kawo muku rahoto kan yadda gwamnatin Ukraine ke neman sojojin sa kai daga kasashen waje domin su kawo wa kasar dauki yayin da Rasha ta mamaye wasu yankunanta.

'Yan Najeriya da dama sun nuna sha'awar kawo dauki, inda suka cika makil a ofishin jakadancin Ukraine da ke Abuja domin bayyana sha'awarsu, kamar yadda The Guardian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Sai kun biya N560k: Ukraine ga 'yan Najeriyan da ke son taya ta yakar Rasha

A daidai lokacin ne kasar ta Ukraine ta ce dole sai 'yan Najeriya sun ba da wani adadi na kudi kafin su samu damar shiga kasar Ukraine.

Sai kun biya N560k: Ukraine ga 'yan Najeriyan da ke son taya ta yakar Rasha

A wani labarin, ofishin jakadancin Ukraine a Najeriya ya ce 'yan Najeriya da ke son zuwa Ukraine don yakar sojojin Rasha dole ne su amince da biyan dala 1,000 (kwatankwacin N560,000) kowannen saboda a samar musu da tikiti da biza.

Ofishin Jakadancin ya bayyana haka ne a lokacin da ‘yan sa kai daga Najeriya suka yi dandazo a harabarta a Abuja ranar Alhamis domin bayyana shirinsu na shiga Ukraine da Rasha, inji rahoton Leadership.

Sakatare na biyu a ofishin jakadancin Ukraine a Najeriya, Bohdan Soltys, ya tabbatar da cewa kowane dan Najeriyan da ke son zuwa Ukraine zai biya dala 1,000.

Asali: Legit.ng

Online view pixel