Da duminsa: Jirgin jigilar yan Najeriya mazauna Ukraine na biyu ya dira birnin tarayya Abuja

Da duminsa: Jirgin jigilar yan Najeriya mazauna Ukraine na biyu ya dira birnin tarayya Abuja

  • Gwamnatin tarayya na cigaba da jigilar yan Najeriya da yaki ya rutsa dasu a kasar Ukraniya
  • Tun lokacin da yakin ya barke, wasu sun gudu Romania, Hungary, Slovakia da Poland don neman mafaka
  • Yau kwana tara kenan ana cigaba da gwabza yaki tsakanin kasar Rasha da Ukraine

FCT Abuja - Jirgin jigilar dalibai da yan Najeriya mazauna kasar Ukraine na biyu ya bira birnin tarayya Abuja da yammacin Juma'a, 4 ga watan Maris, 2022.

Jirgin Air Peace dauke da yan Najeriyan ya dira tashar Nnamdi Azikiwe misalin karfe 6:35 na yammacin nan, rahoton ChannelsTV.

Wannan shine kashi na biyu na yan Najeriya da aka kwaso daga Ukraine.

Jirgin
Da duminsa: Jirgin jigilar yan Najeriya mazauna Ukraine na biyu ya dira birnin tarayya Abuja Hoto: ChannelsTV
Asali: Facebook

Da safe mun kawo muku cewa yan Najeriya da aka kwaso a yayin da ake tsaka da yakin Rasha da Ukraine sun iso babbar birnin tarayya, Abuja.

Kara karanta wannan

Sai kun biya N560k: Ukraine ga 'yan Najeriyan da ke son taya ta yakar Rasha

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sun isa filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da misalin karfe 7:11 na safiyar yau Juma’a, 4 ga watan Maris, a jirgin Max Air.

Jaridar The Nation ta kuma rahoto cewa gwamnatin tarayya za ta baiwa kowannen su dala 100.

Dalilin da yasa aka jinkirta jigilar yan Najeriya da yaki ya ritsa da su a Ukraine ranar Alhamis

A gefe guda, mun kawo a baya cewa dalilin da ya sa gwamnatin tarayya ta jinkirta jigilar yan Najeriya mazauna Ukraine zuwa gida ranar Alhamis kamar yadda akayi alkawari ya bayyana.

Daily Trust ta ruwaito wani babban jami'in gwamnati da cewa wasu cikin wadanda ake kokarin jigila sun ki hawa jirgi saboda basu son dawowa Najeriya.

Tun lokacin da yakin ya barke, wasu sun gudu Romania, Hungary, Slovakia da Poland don neman mafaka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel