Bayan janyewar dakarunta, Amurka za ta koma tattaunawa da Taliban a mako mai zuwa

Bayan janyewar dakarunta, Amurka za ta koma tattaunawa da Taliban a mako mai zuwa

  • Bayan janyewar dakarun Amurka a kasar Afghanistan, hukumomin Amurka za su koma tattaunawa da Taliban
  • Wannan tattaunawar za ta zo ne a mako mai zuwa, kuma za a yi ta ne a kasar Qatar da wakilin Amurka da na Taliban
  • Daga cikin batutuwan da za a tattuna, akwai batu kan abin da ya shafi da ta'addanci da ayyukan jin kai a Afghanistan

Afghanistan - Channels Tv ta ruwaito cewa, kasar Amurka za ta koma tattaunawa da kungiyar Taliban a mako mai zuwa a kasar Qatar, inda za ta tattauna da wasu batutuwan da suka shafi yaki da ta'addanci da kuma jin kai a Afganistan.

Wakilin Amurka na musamman a Afganistan, Tom West, zai jagoranci tawagar Amurka domin tattaunawa ta tsawon makonni biyu, in ji kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka Ned Price a jiya Talata.

Read also

Gwamnati ta fara rabawa talakawa kudi N1.6bn a jihar Jigawa

Tattaunwar Amurka da Taliban | Hoto: aljazeera.com
Amurka za ta ci gaba da tattaunawa da Taliban a mako mai zuwa
Source: UGC

Bangarorin biyu za su tattauna kan muhimman muradan kasa wadanda suka hada da ayyukan yaki da ta’addanci a kan kungiyar IS da Al-Qaeda, da taimakon jin kai, da tattalin arzikin Afghanistan da ya lalace.

Hakazalika za a tattauana kan ficewar Amurkawa cikin aminci ga ‘yan kasar Amurka da ‘yan Afghanistan da suka yi wa Amurka aiki a lokacin mamayar shekaru 20.

West, wanda ya maye gurbin Zalmay Khalilzad a matsayin a watan Oktoba, kwanan nan ya gana da wakilan Taliban a Pakistan a farkon Nuwamba, inji rahoton Aljazeera.

An gudanar da zama na farko tsakanin bangarorin biyu a ranakun 9 zuwa 10 ga watan Oktoba a Doha babban birnin Qatar, inda jami'an diflomasiyyar Amurka da ke sa ido kan hulda da kasar Afghanistan suka mika wuya bayan kwace iko da kungiyar Taliban tayi.

Read also

Akwai yiwuwar kasar Amurka ta garkamawa Najeriya takunkumin sayen kayan yaki

West a ranar Juma'a ya sake nanata sharuddan Amurka ga Taliban na samun tallafin kudi da diflomasiyya na Amurka: yaki da ta'addanci kafa gwamnatin hadin kai, mutunta 'yancin tsiraru da mata, da samar da damammakin samun ilimi da aikin yi.

Ya ce Amurka za ta ci gaba da tattaunawa da Taliban kuma a halin yanzu tana ba da agajin jin kai ne kawai ga kasar.

Amir Khan Muttaqi, ministan harkokin wajen gwamnatin Taliban, wanda kasashen duniya ba su amince da shi ba, ya yi kira a makon da ya gabata a wata budaddiyar wasika ga majalisar dokokin Amurka kan sakin kadarorin Afghanistan da Amurka ta daskarar.

Taliban ta haramta kida a Afghanistan, an sanya wa mata sabuwar doka

A baya kunji cewa, Kungiyar Taliban ta bayyana cewa za ta tabbatar da haramta kida a Afghanistan saboda "Ba Musulunci ba ne".

Wannan batu na kunshe ne a cikin wata hira da jaridar New York Times da kakakin kungiyar Taliban, Zabiullah Mujahid, a ranar Alhamis 26 ga watan Agusta, Ripples Nigeria ta ruwaito.

Read also

Gwamnatin Tarayya ta amincewa kamfanonin wuta su kara kudin shan lantarki a 2021

Sai dai ya lura cewa Taliban na fatan shawo kan mutane su yi biyayya ga sabuwar dokar, maimakon tilasta musu.

Source: Legit Newspaper

Online view pixel