Gwamnati ta fara rabawa talakawa kudi N1.6bn a jihar Jigawa

Gwamnati ta fara rabawa talakawa kudi N1.6bn a jihar Jigawa

  • Shirin CCT na rabon dubu biyar-biyar ga gajiyayyu a fadin ya cigaba da gudana a jihar Jigawa
  • Gwamnatin tarayya ta kaddamar da wannan shiri a shekarar 2016 don taimakawa marasa karfi
  • Sama da mutum 160,000 zasu amfani da kudi sama da bilyan daya da rabi da za'a raba a Jigawa

Jigawa - Gwamnatin tarayya ta dawo rabon kudi N5,000 na shirin CCT na ma'aikatar jinkai da walwalan jama'a ga al'ummar Jihar Jigawa ranar Juma'a, 20 ga Nuwamba, 2021.

Leadership ta ruwaito cewa jama'a sun yi gangami a wuraren bada kudi a karamar hukumar Kiyawa ta jihar.

A cewar rijistan rabon kudin, sama da talakawa mutum 167,620 ake sa ran zasu samu rabonsu cikin N1.6 billion.

Rahoton ya kara da cewa mutane sun tafi wajen da katunansu domin karban kudi.

Kara karanta wannan

Shugaban Najeriya Buhari zai ba Gwamnoni 36 bashin Naira Biliyan 650 da za a karba a 2051

Gwamnati ta fara rabawa talakawa kudi N1.6bn a jihar Jigawa
Gwamnati ta fara rabawa talakawa kudi N1.6bn a jihar Jigawa
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daya daga cikin wadanda suka amfana da kudi, Hajara Rabi'u ta bayyanawa manema labarai farin cikinta game da wannan kudi.

A jawabin da ta yiwa Leadership:

"Na tsufa da yin wani aiki, abinda nike bukata yanzu shine kudin abinci na sauran ranakun da zan yi a duniya, nagode Allah wannan N5,000 zai taimaka min."

Jami'in yada labarai da horo na jihar, Malam Mustapha Yakubu Madobi, ya ce wannan kudi da ake biya yanzu na watan Mayu da Yuni ne.

Ya kara da cewa Gwamnatin tarayya ta baiwa wasu kamfanoni biy kwangilan biyan kudin kuma kamfanin farko ya biya mutane 67,402 yayinda dayan kamfanin zai biya sauran mutum 91,255 a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel