Akwai yiwuwar kasar Amurka ta garkamawa Najeriya takunkumin sayen kayan yaki

Akwai yiwuwar kasar Amurka ta garkamawa Najeriya takunkumin sayen kayan yaki

  • Babu mamaki kasar Amurka ta hukunta gwamnatin Najeriya a dalilin zargin cin zarafin farar hula
  • Dokar Amurka zata hana a saidawa Najeriya makamai muddin sojojin kasar su na wuce gona da iri
  • Ana zargin jami’an tsaro da yi wa masu zanga-zanga kisan kiyashi a lokacin rikicin #EndSARS

Jaridar Punch tace duk da yadda ake fama da matsalar rashin tsaro a Najeriya ta na fuskantar barazanar takunkumin sayen makamai daga kasar Amurka.

Hakan na zuwa ne a sakamakon rahoton kwamitin da ya yi bincike a kan tarzomar da ta biyo bayan zanga-zangar EndSARS da ya zargi sojoji da kisan gilla.

Rahoton da kwamitin ya gabatar ya jefi jami’an tsaro da zargin hallaka wasu masu zanga-zanga a kofar shiga unguwar Lekki, jihar Legas a watan Oktoban 2020.

A halin yanzu, kasar Amurka, Birtaniya, majalisar dinkin Duniya da kungiyar Amnesty ta fara huro wuta cewa a aiwatar da shawarwarin da kwamitin ya bada.

Kara karanta wannan

EndSARS: Bayan shekara 1, bincike ya tona abin da ya faru a Lekki, an zargi Soji da kisan kiyashi

Akwai dokar Leahy a Amurka wanda ta ke lura da yadda sojojin Najeriya su ke amfani da makamai domin a hana jami’an tsaro zaluntar masu farar hula.

Kayan yaki
Jirgin Super Tucano na Amurka Hoto: www.airforce-technology.com
Asali: UGC

Dokar ta taba kawo cikas a baya

Kafin yanzu gwamnatin Amurka tayi amfani da dokar, ta hana a saidawa Najeriya makamai ko a ba ta gudumuwa saboda wuce gona da irin jami’a tsaron na ta.

A lokacin da Goodluck Jonathan yake mulki ne gwamnatin Barack Obama ta kakabawa Najeriya wannan takunkumi, duk da ana tsakiyar yaki da Boko Haram.

Bayan Donald Trump ya karbi mulki a karshen 2016, ya cire wannan takunkumi, kuma har an saidawa Najeriya jiragen yakin Super Tucano masu barin wuta.

Duk da haka, Amurka ta gargadi gwamnatin tarayya cewa ana sa ido a kan abin da sojoji suke yi. The Cable tace a halin yanzu Najeriya na iya tsokano fushin kasar.

Kara karanta wannan

Jami'ar Ilorin ta kori dalibin dan aji hudu da ya lakadawa lakcararsa dukan kawo wuka

Gwamnatin Najeriya ta na fuskanatar barazana

A farkon shekarar nan, Reuters ta rahoto cewa majalisar Amurka na tunanin dawo da wannan takunkumi. Kungiyar Amnesty tana cikin masu neman a yi haka.

Jami’in kungiyar Amnesty Intl, Adotei Akwei ya aika takarda ya na neman gwamnatin Amurka ta hana Najeriya makamai saboda sojoji na cin zarafin al’umma.

Haka zalika jam'iyyar PDP ta na rokon sakataren gwamnatin Amurka ta binciki wannan zargi. Hakan dai zai iya kawo cikas wajen yaki da ake yi da 'yan bindiga.

Kudin shan lantarki zai tashi a Disamba

A makon nan ne rahotanni suka zo mana cewa gwamnatin tarayya ta hannun NERC, ta amincewa kamfanoni su kara farashin shan wutar lantarki a Najeriya.

Idan an yi karin wutan, babu makawa sai farashin sayen lantarki zai kara tsada. Haka zalika ana ta raba na’urori domin mutane su rika biyan kudin wutan da suka sha.

Kara karanta wannan

Abubuwa 17 da ya kamata ku sani a rahoton da kwamitin Endsars ya gabatar

Asali: Legit.ng

Online view pixel