Gwamnatin Tarayya ta amincewa kamfanonin wuta su kara kudin shan lantarki a 2021

Gwamnatin Tarayya ta amincewa kamfanonin wuta su kara kudin shan lantarki a 2021

  • Gwamnatin tarayya ta NERC ta amincewa kamfanonin raba wuta su sake duba farashin shan lantarki
  • Akwai yiwuwar kamfanonin lantarki su kara kudi bayan zaman da za ayi a watan Disamba mai zuwa
  • Hukumar NERC ta ba kamfanoni damar canza farashi a kai-a kai, la’akari da halin da kasuwa ta ke ciki

Abuja - Masu amfani da wutar lantarki za su ga sauyi a watan Disamban shekarar nan bayan gwamnatin tarayya ta kawo sauyi a farashin shan wuta.

Punch tace akwai yiwuwar mutane su rika biyan kudin lantarkin da ya fi na da, a sakamakon karin da aka ba kamfanonin raba lantarkin su yi a Disamba.

NERC mai sa ido a kan harkar wuta a Najeriya za ta fito da sabon tsarin farashi a watan Disamba, sai dai idan wani abu da ya bijiro ya hana hukumar cikas.

Kara karanta wannan

Rikicin VAT: Gwamnatin Buhari na tunanin sasantawa da Wike da Gwamnonin Kudu ta huta

Hukumar za ta zauna a Disamban 2021 domin a tattauna a kan wasu abubuwa da suka ta’allaka da samar da wutar lantarki da kuma raba shi ga al’umma.

Kamfanoni za su iya kara kudin wuta bini-bini?

Doka ta bada dama a rika duba farashin wutar lantarki duk bayan watanni shida zuwa shekara biyar domin ganin ko an samu wasu ‘yan canji a kasuwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Lantarki
Tashar wutar lantarki Hoto: technologymirror.com.ng
Asali: UGC

Ana bukatar a sake duba farashin saida lantarkin domin kamfanoni su iya cin riba a kasuwancinsu.

NERC ta yi kira ga masu korafi ko bayanai su gabatar da takardunsu nan da makonni uku. An bada sanarwar ne a ranar Talata, 16 ga watan Nuwambaa, 2021.

Za a raba na'urorin auna shan wuta miliyan 4

Rahoton Inside Business yace hakan na zuwa ne a lokacin da gwamnatin tarayya ta fara shirin raba na’urorin auna shan wuta miliyan hudu a fadin Najeriya.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Gwamnatin Buhari za ta saka sabon haraji, 'Pure Water' zai koma N50 nan kusa

Babban jami’in hukumar NERC, Mista Shittu Shuaibu ya yi magana a wani gidan rediyo a Abuja, yace wannan shi ne sahu na biyu na tsarin NMMP da aka kawo.

“Za a aiwatar da shirin a sahu uku, an kammala sahun farko a karshen Oktoba. An fara sahu na biyu, gwanati za ta raba na’urori miliyan hudu.” – Shuiabu.

Samuel Ortom ya roki Buhari

Gwamnan Benuwai, Samuel Ortom ya roki Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ki rattaba hannu a kan sabon kudirin dokar zabe da majalisa za ta kawo masa.

A wara hira da aka yi da shi, Ortom ya bayyana yadda aka yi Dr. Iyorchia Ayu ya zama shugaban jam'iyyar PDP na kasa, da kuma rawar da Sanata David Mark ya taka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel