Yadda dan Najeriya ya zama sanata a Turai, ya kware a girki, kuma yake so ya gaji Buhari

Yadda dan Najeriya ya zama sanata a Turai, ya kware a girki, kuma yake so ya gaji Buhari

  • Wani dan Najeriya mai suna John Abraham Godson wanda ya kafa tarihi a matsayin sanata bakar fata na farko a kasar Poland ya nuna bajintarsa
  • Tsohon sanatan na kasar Poland duk da cewa yana da digiri na farko, digirin mastas guda 4 da digirin digirgir 2 cikin alfahari ya nuna kwarewarsa a girki
  • John wanda ya zama dan kasar Poland a shekara ta 2001 ya bayyana cewa dafa abinci daya ne daga cikin abubuwan da yake so a rayuwarsa

Poland - John Abraham Godson shi ne shaidar labarin cewa 'yan Najeriya za su iya jagoranci kuma su yi fice a duk kasar da suka tsinci kansu a ciki a duniya.

John wanda ya kafa tarihi a matsayin sanata bakar fata na farko a Poland za a iya yanke cewa kwararre ne idan aka yi la’akari da gogewarsa da nasarorin da ya samu.

Read also

Ra'ayi: Bidiyon matashin da ya bar sana'a ya koma zaman don kallon jiragen kasa

Dan Najeriyan wanda ya zama dan kasar Poland a 2001 kwanan nan ya nuna daya daga cikin muhimman abubuwan da yake sha'awa.

Sanata a turai, mai burin zama shugaban kasa
Sanata a turai: Ga wani dan Najeriya mai sanar girki dake burin gadon Buhari 2023 | Hoto: John Abraham Godson
Source: Facebook

Yana cin abincinsa a matsayin mai sana'ar girki a Poland

A wani rubutun da yayi a dandamalin Facebook na Home4foods, John ya bayyana cewa babban abinda yake sha'awa shine dafa abinci.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

John a lokacin da yake yada hotuna sanye da rigar girkinsa na musamman ya nuna irin ilimin da ya hada.

Mutumin haifaffen Umuahia yana da sana’o’i da dama a karkashin sunan Godson Group.

Zuwa yanzu ya rubuta littattafai guda 15.

Wasu daga cikin nasarorin siyasarsa

Idan ana magana a kan siyasar kasar Poland, John yayi kokari iyakar gwargwadonsa.

BlackPost ya fitar da rahoton cewa, ya lashe kujera a majalisar birnin Łódź wanda ya sanya shi zama bakar fata na farko da aka zaba a ofishin gwamnati a Poland.

Read also

Shugabancin 2023: Gwamna Umahi ya magantu a kan fastocin yaken neman zabensa da suka bayyana

An kuma sake zabarsa a majalisar birnin tare da sakamako mafi kyau na biyu a cikin shekara ta 2010.

Hakazalika an sake zabarsa a shekarar 2011. Yana kuma fatan zama shugaban kasar Najeriya a zaben 2023.

Martanin jama'a a kafar Facebook

Rowland Okereke ya ce:

"Amma ba mu ga tsarin abincin da ka yi ba....Shi ne abin da muke nema a nan ba kai da shugaban kasa ba...Na gode."

Omeye Chukwudi Emmanuel ya ce:

"Yallabai, yanzu na shiga dukkan dandamalin ka, ina fatan in koyi abu daya ko biyu daga gare ka. Ina kan kafa masana'antar bulo da siminti don kera bulo da sayar da kayan gini. Na gode."

Uju Clare ya ce:

"Na taya ka murna yallabai.
"Amma ina neman abincin da zan suma ne bayan na ci, da fatan abincin ka zai sa na suma sosai cikin kwanciyar hankali."

Prisca Jackson ya ce:

"Wow!. Yayi kyau!. Allah ya kara maka albarka da nisan kwana da lafiya."

Read also

Bidiyon ango da ya fashe da kuka yayin da yake taka rawa tare da mahaifiyarsa a wajen bikinsa

Ruwan kudi: Bidiyon yadda wasu mutane suke ta kwasar kudade a kan titi a Amurka

A wani labarin na daban, wata motar kudi a Amurka ta haifar da wani babban al'amari yayin da daya daga cikin kofofinta ta bude kuma kudade daloli masu yawa suka watse a kasa.

Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, 19 ga watan Nuwamba, inda ya kawo tsaiko ga cunkoson jama’a a California, yayin da jama’a ke tururuwa domin kwasar rabonsu.

Da take nadar bidiyon lamarin, wata budurwa mai suna Demi Baby a shafin Instagram ta ce wannan shi ne mafi girman abin mamaki da ta taba gani.

Source: Legit

Online view pixel