Sharif Lawal
8047 articles published since 17 Fab 2023
8047 articles published since 17 Fab 2023
Wata majiya daga Iran ta bayyana cewa Amurka ta amince ta saki kadarorin Iran da aka rike a Qatar. Jami'in gwamnatin Amurka ya yi magana kan lamarin.
Sabon jagoran addini na kasar Iran, Mojtaba Khamenei ya samu raunuka a hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kai. Majiyoyi sun yi magana kan lafiyarsa.
Manyan wakilan gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta Iran sun isa kasar Pakistan don tattaunawa da Amurka kan yakin da aka tsagaita wuta kansa a Gabas ta Tsakiya.
'Yan bindiga dauke da makamai sun kai hari a jihar Imo. Tsagerun 'yan bindigan sun hallaka wani basarake tare da jami'an 'yan sanda yayin harin da suka kai.
Dakarun sojojin Najeriya sun ba hammata iska a tsakaninsu yayin ziyarar da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kai a jihar Bayelsa da ke yankin Kudu maso Kudu.
Shugaban majalisar dokokin Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf, ya gindaya sharuddan fara tattaunawa da Amurka. Ya ce dole sai an cika su kafin a fara tattaunawa.
Tsohon shugaban jam'iyyar APC a jihar Jigawa, Ado Kiri, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar. Ya nuna godiyarsa kan damar da aka ba shi ta kasancewa a jam'iyyar.
Gwamnatin jihar Bauchi ta tashi tsaye don dakile matsalar ayyukan 'yan bindiga. Gwamnatin ta rufe wasu kasuwanni da ake sayar da shanu a kananan hukumomi hudu.
'Yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a jihar Plateau. Tsagerun 'yan bindiga sun kashe mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba.
Sharif Lawal
Samu kari