Dalilin Cire Sunana Daga Ministocin Tinubu 2027 ce Ba Maganar Tsaro ba, Okotete

Dalilin Cire Sunana Daga Ministocin Tinubu 2027 ce Ba Maganar Tsaro ba, Okotete

  • Stella Okotete ta yi karin haske a kan yadda aka yi mata bukulun zama minista a gwamnatin Najeriya
  • ‘Yar siyasar ta ce hassada da kyashi suka sa aka ki na’am da sunanta, ba saboda wata barazanar tsaro ba
  • Idan da akwai zancen tsaro, Okotete ta ce babu ta yadda za a bari ta zama Darekta a bankin NEXIM

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

FCT, Abuja - Stella Okotete tayi magana watanni kimanin shida bayan an hana ta zama minista a gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.

Stella Okotete wanda Darektar cigaban kasuwanci ce a bankin NEXIM ta dauko maganar da aka yi hira da ita a wani shirin yanar gizo.

Stella Okotete
An hana Stella Okotete zama Minista a Majalisa Hoto: Nigerian Senate/stellaokotete.com
Asali: Facebook

Ministoci: An cire sunan Okotete da wasu

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya tsoma baki, ya bada umarnin a saki matar da ta jagoranci zanga-zanga a Arewa

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bada sunan wannan mata da nufin ta zama minista, kuma ta je majalisar dattawa an tantance ta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da sunayen wadanda aka amince da su ya fito, sai aka fahimci Sanatoci sun jefar da Okotete, Nasir El-Rufai da Abubakar Danladi.

A hirar da aka yi da ita a shirin “Mic on Podcast” ranar Asabar, ‘yar siyasar ta ce ba matsalar tsaro ta sa aka gaza yarda da ita ba.

Keyamo ya canji Okotete a gwamnati

Okotete ta ke cewa makircin siyasa kawai tayi aiki a kan ta, aka ki yarda ta zama minista, a karshe aka canza ta da Festus Keyamo.

Tsohuwar shugabar matar ta APC take cewa idan da ta kasance barazanar tsaro, ba za ta cigaba da rike kujerar Darekta a NEXIM ba.

Kara karanta wannan

Babban Labari: Tinubu ya bada umarnin fito da metric tan 102, 000 na masara da shinkafa

Okotete ta ce babu wata hukumar tsaro da ke bincikenta, The Cable ta kawo labarin.

Lissafin zaben 2027 ya hana Okotete ta zama Minista

Bugu da kari, Okotete ta ce masu yakarta sun taso ta a gaba ne saboda tunanin za ta nemi takarar gwamnan jihar Delta a zaben 2027.

"Mafi yawan masu fada da Stelle Okotete a yau duk hassada ce. A watan Afrilu zan cika shekaru 40."
"A shekara 40, wanene zai ce ya ratsa duk matakan gwamnati; karamar hukuma, jiha zuwa tarayya?"
"Ina shekara 36 na zama shugaban matan APC na kasa kuma Darekta mai iko a bankin NEXIM."
"Babu macen da ta rike mukamai biyu lokaci guda. Duk hassada ce, na fahimci abin da su ke tsoro."

- Stella Okotete

Gwamnan bankin CBN

Ana da labari Hon. Aliyu Sani Madakin-Gini ya nemi gwamnan CBN, Yemi Cordoso ya yi bayanin hikimar kai wasu ma’aikata Legas.

Kara karanta wannan

An shiga rudani kan batun mutuwar babban basarake a Najeriya, an fadi gaskiyar abin da ya same shi

A cewarsa babu wata amsa da Gwamnan CBN ya bada kan dauke sassan Abuja da karyewar Naira yayin da ake zarginsa da kabilanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng