Wani Jigo a APC Ya Gargadi Gwamnati, Bai So Ayi wa Ma’aikata Karin Albashi Sosai

Wani Jigo a APC Ya Gargadi Gwamnati, Bai So Ayi wa Ma’aikata Karin Albashi Sosai

  • Osita Okechukwu yana da ra’ayin da ya sha bam-bam da na kungiyoyin kwadago da ‘yan kasuwa
  • ‘Dan siyasar da yana cikin jagorori a APC ya ce bai kamata a laftawa ma’aikata albashi a irin yanzu ba
  • Tsoron Okechukwu shi ne karin albashin zai jawo tashin farashi bayan yadda ake kukan tsadar kaya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Osita Okechukwu wanda yana cikin manya a jam’iyyar APC, ya tsoma baki a game da shirin karin albashin ma’aikata.

Premium Times ta ce Osita Okechukwu ya fitar da jawabi na musamman a ranar Lahadi, yana mai kira ga gwamnatin kasar.

Karin albashi
Bola Tinubu zai yi karin albashi Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Kuskuren karin albashi a 1972

Tsohon shugaban na hukumar VON ya tuna da kuskuren da ya ce kwamitin Jerome Udoji ya yi a mulkin Yakubu Gowon a 1972.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Gwamnatin Kano ta cika alkawari, ta dira kan rumbun ajiyar masu boye abinci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jerome Udoji ya bada shawarar ayi wa ma’aikata karin albashi a lokacin da aka samu kudi, a karshe hakan ya jawo matsala.

Wasu suna ganin daukar shawarar Udoji da gwamnatin soja tayi ya haifar da hauhawar farashi wanda ana kuka da shi yau.

Karin albashi ko karin tsadar kaya?

"Ra’ayin da na dauka shi ne shakka-babu, yin kari mara tsari zai jagwagwala matsalar hauhawar farashin da mu ke da shi a kasar."

- Osita Okechukwu

'Yan kwadago za su hakura da karin albashi?

Mr Okechukwu yana so ‘yan NLC da TUC su hakura da maganar zuwa yajin-aiki, su goyi bayan tsare-tsaren gwamnatin Bola Tinubu.

Mai girma Bola Tinubu ya kaddamar da aikin gina gidaje a wasu jihohi, ‘dan siyasar ya ce kyau ‘yan kwadago su marawa shirin baya.

Blueprint ta rahoto Okechukwu yana cewa samar da gidaje miliyan guda ga ma’aikata ya fi alheri a kan kara kudi da ake karba.

Kara karanta wannan

APC tayi maganar yunkurin dawo da Sanusi II gidan sarauta da rushe masarautun Kano

A karshe, ‘dan siyasar ya bada shawarwarin yadda ma’aikata za su mallaki gidaje a saukake bayan cire tallafin fetur da aka yi a 2023.

Ana sa ran kwamitin Goni Aji da aka rantsar a watan nan zai saurari wannan zance.

NLC da TUC na neman karin albashi

Zuwa yanzu kungiyoyin NLC da TUC sun huro wuta cewa dole ayi wa ma’aikata karin albashi sosai saboda karyewar kimar Naira.

Dama can 'yan kwadago sun yi barazanar durkusar da kasar idan ba a biya masu bukatunsu ba, su na kukan rayuwa ta kara tsada.

Asali: Legit.ng

Online view pixel