Ka Shiga Uku: Wike Ya ci Mutuncin Atiku a Taro Tun da Obasanjo Ya Goyi Bayan Obi

Ka Shiga Uku: Wike Ya ci Mutuncin Atiku a Taro Tun da Obasanjo Ya Goyi Bayan Obi

Nyesom Wike ya sake dura kan Atiku Abubakar da wasu habaici da ya yi a wajen kaddamar da titi

Gwamnan Ribas yana ganin akwai matsala muddin Obasanjo ba zai goyi bayan takarar Atiku ba

Atiku Abubakar shi ne mataimakin shugaban kasa a lokacin da Obasanjo yake rike da mulkin Najeriya

Rivers - Gwamnan jihar Ribas watau Nyesom Wike, ya caccaki Atiku Abubakar a sakamakon goyon bayan Peter Obi da Olusegun Obasanjo yake yi.

The Cable ta rahoto Gwamna Nyesom Wike yana magana a kan mubaya’ar da tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya yi wa ‘dan takaran LP.

Da yake bayani wajen bude titin da gwamnatinsa ta gina a karamar hukumar Emohua, Wike ya ce da matsala idan Obasanjo bai tare da Atiku.

Gwamnan yake habaici ya ce muddin Obasanjo da Atiku sun yi aiki tare na tsawon shekaru, bai dace ya goyi bayan takarar wani dabam a zabe ba.

Kara karanta wannan

Abin da Ya Faru da Atiku a Zaben 2019 Bayan Obasanjo Ya Marawa Takararsa Baya

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Akwai matsala kenan - Gwamna Nyesom Wike

“Na yi aiki da wani na shekaru takwas, mu na amfani da wannan cewa mun yi kokari a ofis domin mu yi kamfe.
Sai kuma mai gidana ya goyi bayan wani mutum dabam, ba ni ba? Akwai babbar matsala a wani wurin.
Ka je ka kama mai gidanka wanda yake goyon bayan wani mutumin da ba kai ba.”

- Nyesom Wike

Wike da Peter Obi
Gwamna Nyesom Wike da Peter Obi Hoto: @GovWike
Asali: Twitter

Da ma Obasanjo ya yi gum da bakinsa

A ranar Litinin, Daily Trust ta rahoto Wike yana cewa ya so a ce Obasanjo bai tsoma baki a kan wanda yake goyon baya ya zama sabon shugaban Najeriya ba.

A wajen ne Gwamnan ya musanya zargin da ake yi masa na tsoma baki a aikin kwamitin Samuel Ortom da ya raba gardamar yankin da za a ba takara a PDP.

Kara karanta wannan

Abin da Obasanjo Ya Fada Game da Masu Neman Mulki Yayin da Ya Fito da 'Dan takara

"Na yi addua ka da Obasanjo ya ce uffan ba. Lokacin da na ga wasika a daren da ya wuce, abin ya girgiza ni. Idan mai gidanka bai tare da kai, akwai matsala.
Kun je ku na lallabar mai gidanka domin ya goyi bayanku. Mai gidanka ya dauki lokaci, sai kuma ya fitar da wasika ya ce a goyi bayan wani ‘dan takara dabam.

- Nyesom Wike

Goyon bayan 2019 ya yi tasiri?

Kun samu labari cewa Olusegun Obasanjo yana tare da Peter Obi a zaben shekarar nan, amma babu tabbacin cewa hakan zai ba Jam’iyyar LP ko da a jiharsa.

A zabukan 2019, Cif Obasanjo ya goyi bayan Atiku Abubakar, duk da haka Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC ya ba shi ratar kuri’u fiye da 87, 000.

Asali: Legit.ng

Online view pixel