'Yan bindiga fiye da 50 sun kai hari ma'aikatar gwamnatin Nasarawa, sun sace wani akwati mai muhimmanci

'Yan bindiga fiye da 50 sun kai hari ma'aikatar gwamnatin Nasarawa, sun sace wani akwati mai muhimmanci

  • 'Yan bindiga kimanin 50 sun kai hari hukumar kananan hukumomi na jihar Nasarawa
  • Yan bindigan sun daure jami'an NSCDC masu tsaron wurin sun kwace bindgarsu AK-47
  • Har wa yau, yan bindigan sun sace wani akwati dauke da abubuwa masu muhimmanci

Nasarawa - A kalla yan bindiga 50 ne suka kutsa hukumar kananan hukumomi na gwamnatin jihar Nasarawa suka sace akwati dauke da abubuwa masu muhimmanci da bindiga Ak-47 mallakar jami'in NSCDC.

Jaridar The Sun ta ruwaito cewa sakataren dindindin na hukumar, Rammatu Julde, ne ta bayyana hakan a Lafia, babban birnin jihar Nasarawa a safiyar Talata.

'Yan bindiga fiye da 50 sun kai hari ma'aikatar gwamnatin Nasarawa, sun sace wani akwati mai muhimmanci
Hukumar kula da kananan hukumomi na Nasarawa. Hoto: The Sun
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yan bindiga sun sake kai hari jami'ar Arewa, Sun yi awon gaba da dalibai

Julde ta ce 'yan bindigan sun kutsa haraban misalin karfe 2 na daren Litinin suka shiga ta babbar kofa da ke sada ofisoshin hukumar kananan hukumomi da na ma'aikatan gwamnati, suka yi karensu babu babbaka, rahoton The Sun.

Julde ta ruwaito cewa:

"Sun kai hari misalin karfe 2 na daren Litinin, yayin harin, sun daure jami'an NSCDC guda biyu da ke tsare wurin sannan suka kwace AK-47 guda daya daga hannunsu.
"Sun yi yunkurin sace babban janareto mai karfin KVA 150 amma ba su yi nasara ba; amma sun sace akwati dauke da abubuwa masu muhimmanci. Yanzu muna bincike don gano sauran abin da suka sace."

Sakataren hukumar ya tabbatar babu wanda ya rasa ransa sakamakon harin ya kuma yi kira ga NSCDC ta gudanar da bincike mai zurfi don tabbatar babu hadin baki tsakanin jami'anta da maharan.

Yan bindigan sun kuma kutsa ofishin hukumar ma'aikatar gwamnatin jihar da ke makwabtaka da hukumar kananan hukumomi inda suka sace manyan talabijin na LED biyu.

Kara karanta wannan

An kashe manoma uku a wani sabon hari da aka kai kan kauyen Filato

Martanin kakakin NSCDC

A bangarensa, kakakin NSCDC, Jerry Victor ya yi bayanin cewa:

"Yan bindigan sun kai hari a harabar hukumar a daren ranar Litinin kuma abin takaici babu wanda ya tanka musu ko yunkurin taka musu birki.
"An daure jami'an mu biyu da ke tsare wurin an karba AK-47 daga hannunsu. Jami'an biyu na tsare a hedkwatar mu da ke Lafia ana bincike."

Lamarin ya faru ne watanni uku bayan wasu yan bindigan sun kai hari ma'aikatar kudi, tsare-tare a Lafia inda suka sace kudi mai yawa ba tare da wani ya taka musu birki ba.

'Yan bindiga sun afka caji ofis, sun sace ƴar sanda da bindigu masu ɗimbin yawa

A wani labarin, kun ji cewa an nemi wata jami'ar 'yan sanda an rasa bayan wasu 'yan bindiga sun kai hari caji ofis da ke Umulokpa a jihar Enugu a karamar hukumar Uzo-Uwani a jihar Enugu.

Kara karanta wannan

Zamfara: A kalla rayuka 12 sun salwanta, 'yan bindiga sun kone motar 'yan sanda

A ruwayar Daily Trust, Rundunar 'yan sandan ta tabbatar a ranar Litinin cewa wata 'yar sanda da ba a bayyana suna ta ba ta bata bayan harin da aka kai a ranar Asabar 9 ga watan Oktoban 2021.

An sace dukkan makaman da ke dajin ajiye makamai a ofishin 'yan sandan an kuma lalata na'urar CCTV da motoccin zuwa aiki na 'yan sandan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel