Zamfara: A kalla rayuka 12 sun salwanta, 'yan bindiga sun kone motar 'yan sanda

Zamfara: A kalla rayuka 12 sun salwanta, 'yan bindiga sun kone motar 'yan sanda

  • Rayuka 12 ne suka sheka lahira sakamakon farmakin da 'yan bindiga suka kai kauyen Sakajiki
  • 'Yan bindigan sun tsinkayi kauyen jihar Zamfaran ne wurin karfe 9 na dare inda suka dinga ruwan wuta
  • Jami'an 'yan sanda sun kokarta wurin dakile harin, sai dai cikin rashin sa'a 'yan bindigan sun fi karfinsu

Zamfara - A kalla rayuka 12 aka kashe yayin farmakin da 'yan bindigan daji suka kai kauyen Sakajiki da ke masarautar Kauran Namoda a jihar Zamfara.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Zamfara, Mohammed Shehu, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga gidan talabijin na Channels a ranar Juma'a.

Ya ce an samu wadanda suka rasa rayukansu yayin aukuwar lamarin kuma ba don taimakon jami'an tsaro ba, da abun ya fi haka muni.

Zamfara: A kalla rayuka 12 sun salwanta, 'yan bindiga sun kone motar 'yan sanda
Zamfara: A kalla rayuka 12 sun salwanta, 'yan bindiga sun kone motar 'yan sanda. Hoto daga channelstv.com
Asali: UGC

A yayin bada labarin yadda lamarin ya faru, wata majiya a kauyen ta sanar da Channels TV cewa miyagun sun bayyana wurin karfe 9 na dare a ranar Alhamis kuma sun dinga zuba ruwan wuta.

Ya kara da cewa a kalla mutum 12 aka tabbatar da mutuwarsu yayin farmakin har zuwa karfe hudu na asubahin Juma'a.

Sun kara da banka wa wasu shaguna da gidaje wuta, har da wani ofishin 'yan sanda tare da ababen hawansu.

Wata majiya ta yi bayanin cewa wadanda aka tabbatar da mutuwarsu su ne wadanda aka ga gangar jikinsu a fili yayin da ake neman wadanda ba a gani ba.

Kamar yadda yace, jami'an 'yan sanda sun yi iyakar kokarinsu wurin dakile harin amma sun kasa saboda yawan 'yan bindigan.

A bangaren Shehu, ya bayyana cewa kwamishinan 'yan sandan jihar Zamfara ya tura jami'ansa domin maganin matsalar.

Ya tabbatar wa da jama'ar yankin cewa rundunar za ta yi duk kokarin da ya dace wurin tabbatar da ganin bayan ta'addanci a jihar.

Mata 6 da kananan yara 9 sun tsero daga hannun Boko Haram

A wani labari na daban, mata shida tare da yara kanana 9 da aka sace a yankin arewa maso gabas sun tsero daga hannun miyagun da suka sace su. Sun kwashe kwanaki shida suna tafiya a daji kafin su samu 'yanci a ranar Litinin.

Mutum 15 din an sace su daban-daban ne a gonakinsu da ke kauyukan Takulashi a Chibok , jihar Borno da kuma Cofure da ke karamar hukumar Hong ta jihar Adamawa watanni da yawa da suka gabata, Channels TV ta wallafa.

Uku daga cikin wadanda aka sacen an kwashe su ne tare da kananan 'ya'yansu biyar yayin wani samame da 'yan ta'addan suka kai Takulashi a watan Oktoban shekarar da ta gabata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel