An kashe manoma uku a wani sabon hari da aka kai kan kauyen Filato

An kashe manoma uku a wani sabon hari da aka kai kan kauyen Filato

  • Manoma uku sun kwanta dama a wani sabon hari da wasu 'yan bindiga suka kai kan kauyen Nkiendonwro da ke yankin Miango a karamar hukumar Bassa ta jihar Filato
  • An tattaro cewa mummunan al'amarin ya afku ne a safiyar Juma'a yayin da mamatan ke a hanyarsu ta zuwa gona
  • Kakakin 'yan sandan jihar ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce an tura jami'an domin dawo da zaman lafiya

Akalla manoma uku ne aka kashe a kauyen Nkiendonwro da ke yankin Miango a karamar hukumar Bassa ta jihar Filato a safiyar ranar Juma’a.

Madison Davidson, kakakin Kungiyar kabilar Irigwe, ya bayyana cewa mamatan na a hanyarsu ta zuwa gona lokacin da suka fada hannun ‘yan bindiga, Daily Trust ta rahoto.

An kashe manoma uku a wani sabon hari da aka kai kan kauyen Filato
An kashe manoma uku a wani sabon hari da aka kai kan kauyen Filato Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Ya ce an kai rahoton lamarin ga shugaban ‘yan sandan karamar hukumar Bassa.

Kara karanta wannan

Hon Sha'aban: Da a yau za a yi zaben gwamna a Kano, warwas za a yi wa APC

Ya ce:

“A yau kabilar Irigwe ta sake wayar gari cikin wani tashin hankali. Abun bakin ciki wadannan mahara na ci gaba da kashe mu sannan suna mamaye kasarmu ta gado, amma babu komai mun mika lamarinmu ga Allah.
“Ya kamata gwamnati da jami’an tsaro su tashi tsaye su gudanar da aikinsu yadda ya kamata don kare mutanen da basu ji ba basu gani ba.”

Da aka kira don jin ta bakin shi, mai magana da yawun yan sandan jihar, ASP Ubah Gabriel, ya tabbatar da lamarin, cewa an tura Jami’an ‘yan sanda don hana ci gaban hare-hare.

A ranar 4 ga watan Oktoba, an kashe mutum uku Sannan an jikkata wasu uku yayin wani hari a kauyen Hukke da ke yankin Miango.

Makiyaya da mutanen Irigwe suna yawan ganin laifin juna kan hare-hare da na ranuwar gayya a kauyukan Bassa.

Kara karanta wannan

Jigawa: An kama makiyayi da shanunsa 73 da awaki 14 saboda kutse cikin gona

Kisan gilla: Jami’an ‘Yan Sanda sun cafko mutane 10 da suka kashe Matafiya a hanyar Filato

A wani labari na daban, mun kawo a baya cewa jundunar ‘yan sanda na jihar Filato, sun gurfanar da wasu mutane 10 da ake zargin su da hannu a kashe wasu Fulani da tafiya ta bi da su ta Jos.

Jaridar Daily Trust tace an hallaka wadannan mutane ne yayin da suka bi ta titin Gada-biyu zuwa Rukuba, garin Jos, a jihar Filato a cikin tsakiyar watan Agusta.

Jami’an tsaron sun gurfanar da wadanda ake zargi da wannan laifi a babban kotun jiha da ke Filato.

Asali: Legit.ng

Online view pixel