'Yan bindiga sun afka caji ofis, sun sace ƴar sanda da bindigu masu ɗimbin yawa

'Yan bindiga sun afka caji ofis, sun sace ƴar sanda da bindigu masu ɗimbin yawa

  • Yan bindiga sun kai farmaki ofishin rundunar yan sanda a Umulokpa a jihar Enugu
  • Maharan sun lalata motocci da na'urar CCTV, sannan sun kwashe dukkan bindigun da ke ofishin
  • Har wa yau, an nemi wata jami'ar 'yan sanda ba a ganta ba bayan da maharan suka tafi

Enugu - An nemi wata jami'ar 'yan sanda an rasa bayan wasu 'yan bindiga sun kai hari caji ofis da ke Umulokpa a jihar Enugu a karamar hukumar Uzo-Uwani a jihar Enugu.

A ruwayar Daily Trust, Rundunar 'yan sandan ta tabbatar a ranar Litinin cewa wata 'yar sanda da ba a bayyana suna ta ba ta bata bayan harin da aka kai a ranar Asabar 9 ga watan Oktoban 2021.

'Yan bindiga sun afka ofishin 'yan sanda, sun sace dukkan bindigu sun kona motocci
Bata gari sun afka ofishin 'yan sanda, sun sace dukkan bindigu sun kona motocci. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun kai hari ofishin yan sanda, sun saki wadanda aka tsare sun kona motocin sintiri

An sace dukkan makaman da ke dajin ajiye makamai a ofishin 'yan sandan an kuma lalata na'urar CCTV da motoccin zuwa aiki na 'yan sandan.

Wane mataki kwamishinan 'yan sanda ya dauka?

Kwamishinan yan sandan jihar, CP Abubakar Lawal, tuni ya bada umurnin sashin CID ya fara bincike kan lamarin domin nemo jami'ar da ta bace tare da kama maharan kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Sanarwar da kakakin yan sanda ASP Daniel Ndukwe ya fitar ta ce CP Lawal ya bada umurnin ne a ranar Litinin yayin da ya ziyarci wurin da abin ya faru.

Ya ce:

"Kwamishinan yan sandan Enugu, CP Abubakar Lawal, fdc, ya bada umurin sashin CID ta tawaga na musamman su tsananta bincike don gano jami'ar da ake nema sannan su binciko bata garin, da suka lalata motocci da wasu kayayyaki a ofishin da ke Umulokpa a karamar hukumar Uzo-Uwani a yammacin 09/10/2021.

Kara karanta wannan

Zamfara: A kalla rayuka 12 sun salwanta, 'yan bindiga sun kone motar 'yan sanda

"Ya bada wannan umurnin ne bayan ya jagoranci tawagar manyan jami'ai da kwamandojin 'yan sanda zuwa wurin da abin ya faru.
"Har wa yau, ana kira ga al'umma, musamman mazauna jihar su taimakawa rundunar da bayanai masu amfani da zai taimaka a kama wadanda suka kai harin.
"Za a sirrinta sunan duk wanda ya taimaka da bayanai, kuma ana iya turawa zuwa da adireshin imel contact042ppro@gmail.com ko a kira 08032003702 ko 08075390883.”

'Yan bindiga sun afka ofishin ƴan sandan Zamfara, sunyi kisa, sun sace bindigu AK-47 masu yawa

A wani labarin daban, wasu ɓata gari da ake kyautata zaton ƴan bindiga ne sun kai hari ofishin yan sanda a Zamfara sun kashe jami'in ɗan sanda ɗaya, rahoton SaharaReporters.

Yan bindiga sun kuma kashe wani shugaban ƴan banga da wasu mutane biyu a garuruwan Nahuce da Gidan Janbula a ƙaramar hukumar Bungudu.

Har wa yau, ƴan bindigan sun yi awon gaba da mutane hudu yayin da suka kawo harin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel