Yanzu-Yanzu: Yan bindiga sun sake kai hari jami'ar Arewa, Sun yi awon gaba da dalibai

Yanzu-Yanzu: Yan bindiga sun sake kai hari jami'ar Arewa, Sun yi awon gaba da dalibai

  • Wasu yan bindiga da ba'a san ko suwaye ba sun sace ɗalibai hudu a yankin Mararaba Akunza, dake karamar hukumar Lafia
  • Rahoto ya nuna cewa ana tsammanin ɗaliban suna karatu ne a jami'ar tarayya ta Lafia, amma hukumar makarantar ta musanta
  • Kakakin yan sandan jihar, ASP Nansel Ramhan, yace hukumar ba ta samu rahoto ba a hukumance

Nasarawa - Wasu yan bindiga sun kai hari yankin Mararaba Akunza dake jami'ar tarayya Lafia, a ƙaramar hukumar Lafia jihar Nasarawa.

Yayin harin yan bindigan sun yi awon gaba da mutum huɗu da ake tsammanin ɗalibai jami'ar ne.

Dailytrust ta rahoto cewa lamarin ya faru ne da misalin 7:00-8:00 na daren ranar Asabar dai-dai lokacin da ake ruwan sama.

Jami'ar Lafiya
Yanzu-Yanzu: Yan bindiga sun sake kai hari jami'ar Arewa, Sun yi awon gaba da dalibai Hoto: Federal University Lafia FB Fage
Asali: Facebook

Wani shaidan gani da ido, wanda ya zanta da manema labarai, yace maharan sun zo da yawansu, inda suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi kafin su sace daliban zuwa wani wuri da ba'a sani ba.

Kara karanta wannan

Yadda yan bindiga ke sako mutanen da suka kama ba tare da biyan kudin fansa ba a Zamfara

Shin yan bindigan sun nemi kuɗin fansa?

Rahoto ya nuna cewa maharan sun tuntubi iyalan waɗanda suka sace ranar Asabar da misalin ƙarfe 11:30 na dare, inda suka nemi a tattara musu miliyan N25m kuɗin fansa.

Mutumin yace:

"Maharan sun zo da yawansu, suka buɗe wuta a cikin iska domin razana mutanen yankin Mararaba Akunza, kafin daga bisani su yi awon gaba da dalibai huɗu."
"Amma babu tabbacin ɗaliban yan jami'ar tarayya dake Lafia ne. Lokacin ana ruwa maharan suka zo ɗauke da bindigun AK-47."
"Kuma sun ɗauki awanni suna aikata mummunan nufinsu, kafin daga baya sun tafi da ɗalibai 4."

Me hukumar makarantar ta faɗa?

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labarai ranar Lahadi, jami'in hulɗa da jama'a na jami'ar, Abubakar Ibrahim, ya musanta rahoton cewa ɗaliban jami'a ne aka sace.

Kara karanta wannan

An kuma, Miyagun yan bindiga sun kutsa fadar Basarake, sun yi awon gaba da shi a jihar Katsina

Yace:

"Babu ko ɗaya daga cikin ɗaliban mu da aka sace, lamarin ya faru ne a wajen jami'ar. Bamu samu rahoto daga kowa ba game da sace ɗan su dake karatu a makarantar mu."

Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?

Kakakin rundunar yan sandan jihar Nasarawa, ASP Nansel Ramhan, yace hukumar yan sanda ta samu labari ne ta dandalin sada zumunta.

A cewarsa duk da basu samu rahoton lamarin a hukumance ba, amma an tura ƙarin jami'an yan sanda yankin domin ɗaukar mataki.

Budu da ƙari yace zuwa yanzun babu wanda aka kama game da lamarin amma yan sanda na cigaba da bincike, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

A wani labarin kuma Kwastam ta kwace jarkoki 1,000 makare da man fetur za'a kaiwa yan bindiga a Katsina

Mukaddashin shugaban NCS reshen Katsina, Wada Chide, yace mutane na amfani da abun hawansu wajen siyo fetur su juye a jarkokin.

Kara karanta wannan

Jami'an yan sanda 34,587 da Jirage 3 zamu tura zaben jihar Anambra, IGP Alkali

Ya kuma yi kira ga mazauna jihar musamman waɗanda ke zaune a kauyukan dake bakin boda su cigaba da kiyaye doka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel