Nasrun Minallah: Dakarun soji sun bude wa yan bindigan da suka tsero daga Zamfara wuta a jihar Neja

Nasrun Minallah: Dakarun soji sun bude wa yan bindigan da suka tsero daga Zamfara wuta a jihar Neja

  • Dakarun sojoji sun mamayi yan bindiga sun buɗe musu wuta a jihar Neja, inda suka hallaka aƙalla mutum 32
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa yan bindigan ne suka fara kaiwa yan sanda hari, kafin sojoji su musu kwantan bauna
  • Wata majiya daga cikin jami'an tsaro ya bayyana cewa an kashe manyan yan ta'adda kuma shugabannin yan bindiga

Niger - Jami'an tsaron haɗin guiwa sun hallaka yan bindiga aƙalla 32 a jihar Neja, waɗanda suka tsero daga Zamfara, kamar yadda PRNigeria ta rahoto.

Wannan ya biyo bayan harin da yan bindigan suka kaiwa jami'an tsaro, inda suka harbe yan sanda 5 har Lahira, waɗanda suka yi kokarin maida martani.

Gumurzun ya faru ne a ƙauyen Bangu Gari, dake ƙaramar hukumar Rafi ta jihar Neja ranar Lahadi, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Read also

Halin da yan bindiga suka jefa mutane tun bayan katse hanyoyin sadarwa a jihar Katsina

Sojojin Najeriya
Sojoji sun yi gumurzu da yan bindigan da suka tsero daga Zamfara a Neja, Sun sheke 32 Hoto: independent.ng
Source: UGC

Wata majiya daga cikin jami'an tsaro ya bayyana cewa wasu yan bindiga da suka fito daga Zamfara saboda ruwan wutan sojoji, sun fara kafa sansani a yankin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Majiyar tace:

"Adadi mai yawa na yan bindigan ɗauke da muggan makamai, ciki harda roket, sun tattaru a yankin bayan tserowa daga sansaninsu dake Danjibga da Munhaye a ƙaramar hukumar Tsafe, jihar Zamfara."

Yan bindigan sun farmaki yan sanda

Rahotanni sun bayyana cewa yan bindigan sun farmaki caji ofi ɗin yan sanda dake Bangu Gari, ƙaramar hukumar Rafi, inda suka hallaka jami'ai 5.

"Nan take bayan samun rahoton faruwar haka jami'an tsaron haɗin guiwa suka nufi wurin domin kai ɗauki."
"A ƙarin karfi kuma sojoji sun yi wa yan ta'addan kwantan bauna yayin da suka yi kokarin tserewa ta hanyar garin Tegina."
"Aƙalla mutum 32 sojojin suka kashe, cikinsu harda shugabanninsu, Karki Buzu da Yalo Nagoshi, yayin da wani babban ƙasurgumin dan ta'addan, Ali Kawaji, ya samu muggan raunuka."

Read also

Da Duminsa: Babban Sarki a Arewa, Dr Shekarau Agyo, ya riga mu gidan gaskiya

A wani labarin kuma Daliban makarantar koyon karatun larabci da Alƙur'ani, sun bayyana ainihin abinda ya faru a shagalin da suka halarta

Ɗaya daga cikin ɗaliban, Nasirudeen Muhideen, yace mutun ɗaya ne ya sha barasa, amma sauran lemun dake kara kuzari suka sha.

Wani bidiyo da ya watsu a kafafen sada zumunta ya nuna yadda malaman makarantar suka azabtar da ɗaliban.

Source: Legit.ng

Online view pixel