"Dalilin da Ya Sa Zai Yi Wahala 'Yan Adawa Su Iya Kayar da Bola Tinubu a Zaben 2027"
- Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ce ayyukan raya kasa da Tinubu ya gudanar za su wahalar da jam’iyyun adawa wajen kayar da shi a zaben 2027
- Wike ya bayyana cewa ayyukan da ake gani a Abuja za su zama hujjar da APC za ta gabatar wa ’yan Najeriya yayin yakin neman zabe
- Ya ce gwamnatin Abuja na shirin kaddamar da manyan ayyuka akalla 10 kafin ranar 16 ga Janairu, 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ce ababen more rayuwa da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta gudanar kadai za su wa yan adawa su sha wahala wajen kayar da shi a zaben 2027.
Wike ya bayyana cewa ayyukan da shugaban kasar ya aiwatar, musamman a fannin gine-gine da samar da ababen more rayuwa, sun ba gwamnatin APC gagarumar hujjar da za ta gabatar wa ’yan Najeriya yayin yakin neman zabe.

Source: Facebook
Ministan ya bayyana hakan ne ranar Talata a Abuja bayan ya duba wasu ayyukan gine-gine da ake gudanarwa a babban birnin kasar, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
Ya dage cewa sauye-sauyen da ake gani a Abuja sun isa su nuna irin kudirin Tinubu na samar da ci gaba a kasar.
Ayyukan Tinubu za su wahal da yan adawa
A cewarsa, yawan ayyukan da aka gudanar karkashin jagorancin Tinubu zai yi wahala ga abokan hamayyarsa su karyata nasarorin da gwamnatin ta samu.
“Don haka, za ku iya gani karara cewa zai yi wahala a kayar da shugaban kasa a yau, saboda abin da ya yi a bayyane yake.
“Kamar yadda na fada muku, wannan shi ne yakin neman zabemmu. Mutane suna tambayar abin da za mu yi amfani da shi wajen yakin neman zabe, amma muna da dimbin ayyukan da ake iya gani a ko’ina.
“Ba zai yiwu mazauna Abuja su ga irin wadannan ababen more rayuwa da muka samar ba, sannan su ce ba su gamsu da ayyukan da shugaban kasa ya yi ba. Ba a samun irin wannan a ko’ina."
- Nyesom Wike.
Ayyukan da Wike ya duba a Abuja
Ministan ya bayyana cewa ayyukan gine-ginen da ake gudanarwa a Abuja na daga cikin nasarorin da gwamnatin Tinubu za ta iya nunawa, yana mai cewa kammala su zai kara fito da tasirin manufofin shugaban kasar.
Daga cikin ayyukan da ya duba akwai gina titin Inner Southern Expressway, wanda ya taso daga zagayen Area 1 zuwa gadojin Games Village.
Ya kuma duba aikin titin Southern Parkway, wanda ya hada titin Oladipo Diya da Ring Road II.
Haka kuma, ya duba aikin titin Arterial Road S1, wanda aka tsara domin hada Ring Road II da tashar hukumar kashe gobara ta FCT ta hanyar yankunan Kaura da Gaduwa.
Wike ya bayyana gamsuwarsa da yadda ake gudanar da ayyukan, musamman titin Southern Parkway, wanda ya ce an samu gagarumin ci gaba a cikinsa cikin kankanin lokaci.
Wike ya yi wa kansiloli alkawari
Kun ji cewa Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya yi alƙawarin ba duk kansilan da ya tabbatar da nasarar APC a mazabarsa Naira miliyan 10.
Ministan ya buƙaci kansilolin da ke Abuja da su ƙara ƙaimi wajen wayar da kan al'umma da kuma haɗa ƙungiyoyin jama'a domin tabbatar da nasarar APC a mazabunsu.
Asali: Legit.ng

