Wata Sabuwa: Jami'an Kwastam sun bude wuta kan jama'a a jihar Katsina

Wata Sabuwa: Jami'an Kwastam sun bude wuta kan jama'a a jihar Katsina

  • Jami'an hukumar kwastam sun buɗe wa jama'a wuta a ƙaramar hukumar Mani ta jihar Katsina
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa jami'an sun bindige mutum ɗaya, inda akai gaggawar kai shi asibiti domin duba lafiyarsa
  • Kakakin yan sandan jihar, Gambo Isah, yace yan sanda na kan bincike don gano kwastam ɗin da suka aikata haka

Katsina - Rahotanni daga jihar Katsina sun tabbatar da cewa jami'an kwastam sun bindige mutum ɗaya a ƙaramar hukumar Mani.

Hukumar yan sanda reshen jihar ta bayyana cewa wanda aka harbe, Auwal Sani, 35, an harbe shi ne a kafarsa, inda daga baya aka kaishi asibiti domin kulawa da lafiyarsa.

Premium times ta rahoto cewa Lamarin ya faru ne lokacin da jami'an kwastam a cikin motar sintiri suka shiga ƙauyen Fadi Gurje dake ƙaramar hukumar Mani, jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Halin da yan bindiga suka jefa mutane tun bayan katse hanyoyin sadarwa a jihar Katsina

Jami'an kwastam
Wata Sabuwa: Jami'an Kwastam sun bude wuta kan jama'a a jihar Katsina Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Shigarsu ƙauyen ke da wuya, sai jami'an na hukumar kwastam ta ƙasa suka bude wuta kan mai uwa da wabi, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wane mataki yan sanda suka ɗauka?

Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Katsina, Gambo Isa, yace jami'ai sun dukufa bincike don gano masu hannu a lamarin daga cikin jami'an kwastam.

Isah ya ƙara da cewa kwamishinan yan sanda na jihar ya yi kira ga al'ummar yankin su kwantar da hankulansu.

Ya kuma roƙi mutanen dake zaune a yankunan da lamarin ya shafa su cigaba da harkokinsu na yau da kullum yayin da yan sanda ke bincike.

Kakakin yan sandan ya ƙara da cewa jami'an yan sanda na aiki kafaɗa-da-kafaɗa da kwastam domin warware matsalar.

Kwastam sun taba kashe mutum 10

Idan baku manta ba, a baya jami'an kwastam sun hallaka mutum 10 tare da jikkata wasu da dama yayin da direban motar sintiri yayi kan jama'a.

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan daba sun yi wa babban jami'in APC duka har ya gigice, sun kona gidansa a jihar Nasarawa

Legit.ng Hausa ta kawo muku cewa direban motar kwastam ɗin ya faɗa kan jama'a ne lokacin da suka biyo ɗan sumogal a ƙaramar hukumar Jibiya.

A wani labarin na daban mun tattaro muku Yadda mata ke amfani da Hijabi wajen safarar muggan makamai ga yan fashi a Najeriya

Wasu mata biyu da jami'an yan sanda suka cafke sun bayyana yadda suke tallafawa yan fashi ta hanyar amfani da Hijabi.

Matan sun bayyana yadda suke ɗaukar bindigu AK-47 daga wani wuri a umarce su kai ta wani wuri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262