Tinubu Ya Sake Daukarwa 'Yan Najeriya Alkawarin da Ya Gaza Cikawa

Tinubu Ya Sake Daukarwa 'Yan Najeriya Alkawarin da Ya Gaza Cikawa

  • Tinubu ya yi alƙawarin samar da wutar lantarki mai ɗorewa da rage tsadar rayuwa idan ya sake samun nasara a zaɓen 2027
  • Ya ce gwamnatinsa za ta tallafa wa ƙananan masana’antu da sana’o’i domin bunƙasa tattalin arziki da samar da ayyukan yi
  • Shugaban ƙasar ya yi wannan alƙawarin ne yayin gangamin APC a Dutse, inda ya sake tuna wa ’yan Najeriya alkawarin inganta wutar lantarki na 2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Jigawa - Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi alƙawarin samar wa ’yan Najeriya ingantacciyar wutar lantarki.

Shugaban kasar ya kuma yi alkawarin ƙarfafa masana’antu da kuma faɗaɗa damar samun ayyukan yi idan aka sake zaɓensa a babban zaɓen 2027.

Tinubu ya yi alkawarin inganta lantarki
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Jaridar TheCable ta ce Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 10 ga watan Nuwamban 2026 yayin gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a Dutse, babban birnin Jihar Jigawa.

Kara karanta wannan

"Karya suke yi": Tinubu ya sake magana kan dawo da tallafin man fetur

Shugaban ƙasar ya ce gwamnatinsa za ta ɗauki matakan rage tsadar rayuwa tare da tabbatar da samar da wutar lantarki mai inganci a faɗin Najeriya.

Tinubu ya yi alƙawarin samar da wutar lantarki

Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta magance matsalolin da suka shafi samar da wutar lantarki, yana mai cewa ba wai cikakken tsarin sayar da kamfanonin lantarki ga ’yan kasuwa ne kawai zai kawo mafita ba.

“Za mu rage tsadar rayuwa. Za mu samar da ingantacciyar wutar lantarki, ba wai cikakken tsarin mayar da komai hannun kamfanoni masu zaman kansu wanda ba ya aiki ba. Za mu samar muku da ingantacciyar wutar lantarki a Najeriya.” In ji shi.

Alƙawarin na zuwa ne a daidai lokacin da wasu jihohi ke fuskantar matsalar ƙarancin wutar lantarki.

Ministan Lantarki, Joseph Tegbe, ya danganta matsalar da ake samu da ayyukan gyara a tashar samar da wutar lantarki ta Egbin, ƙarancin iskar gas da kuma lalata layukan rarraba lantarki.

Kara karanta wannan

Shugaban APC ya fito da magana kan batun Tinubu bai da lafiyar tsayawa takara a 2027

Ya yi alƙawarin ƙarfafa masana’antu

Shugaban ƙasar ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa za ta yi ƙoƙarin bunƙasa masana’antu domin ƙarfafa tattalin arzikin ƙasa da samar da ƙarin ayyukan yi.

Ya ce za a tallafa wa ƙananan sana’o’i da matsakaitan masana’antu domin su faɗaɗa ayyukansu, su ƙara samar da kayayyaki da kuma ɗaukar ma’aikata.

“Za mu ƙarfafa tushen masana’antu a ƙasarmu. Za mu taimaka wa ƙananan sana’o’i da matsakaitan masana’antu. Za mu faɗaɗa damar samun ayyukan yi ga mutanen da ke neman hanyar samun kuɗin shiga na gaskiya.” In ji shi.

Tinubu ya jaddada cewa rage tsadar rayuwa, inganta wutar lantarki da ƙarfafa masana’antu na daga cikin matakan da gwamnatinsa za ta mayar da hankali a kai.

Alƙawarin da ya yi a zaɓen 2023

A lokacin yaƙin neman zaɓen 2023, Tinubu ya yi wa ’yan Najeriya alƙawarin inganta samar da wutar lantarki a ƙasar.

A wancan lokacin, ya bayyana cewa bai kamata ’yan Najeriya su sake zaɓensa ba idan ya gaza cika wannan alƙawari, sai dai idan yana da cikakken bayani kan dalilin da ya sa bai iya yin hakan ba.

Kara karanta wannan

Okowa: Abokin takarar Atiku a 2023 ya bayyana dalilin da ya sa suka raba gari ya koma APC

Sabon alƙawarin da ya yi a Jigawa ya sake mayar da batun inganta wutar lantarki cikin muhimman alkawuran da ya gabatar yayin neman wa’adin mulki na biyu a zaɓen 2027.

Tinubu ya yi alkawarin inganta wutar lantarki
Mai girma Bola Tinubu tare da uwargidansa Remi Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

Tinubu ba zai dawo da tallafin fetur ba

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta dawo da tallafin man fetur ba.

Shugaba Bola Tinubu da ke neman tazarce ya ce gwamnatinsa za ta mayar da hankali wajen tallafa wa manoma da bunƙasa ilimi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng