Mutum ɗaya ne ya sha barasa, Ɗaliban makarantar Qur'ani sun maida martani kan mummunan azabtarwa da Bulala
- Daliban makarantar koyon karatun larabci da Alƙur'ani, sun bayyana ainihin abinda ya faru a shagalin da suka halarta
- Ɗaya daga cikin ɗaliban, Nasirudeen Muhideen, yace mutun ɗaya ne ya sha barasa, amma sauran lemun dake kara kuzari suka sha
- Wani bidiyo da ya watsu a kafafen sada zumunta ya nuna yadda malaman makarantar suka azabtar da ɗaliban
Kwara - Ɗalibin makarantar Musba'uddeen, ta koyon larabci da Alqur'ani a jihar Kwara, ya maida martani kan cin zarafin da hukumomin makarantar suka musu, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Dalibin, Nasirudeen Muhideen, yayin zantawa da malaminsu, yace shi da wasu abokan karatunsa ne suka je taron shagalin bikin ranar haihuwa.
Amma a bayaninsa, mutun ɗaya daga cikinsu ne ya dirki barasa yayin da sauran suka sha Malta Guinness da kuma lemun ƙara kuzari, wadanda basa cutarwa.
Hukumar makaranta ta kira taron gaggawa kan hoton bidiyon da ya watsu, wanda ya bayyana yadda aka ci mutuncin ɗaliban da bulala, lamarin da ya mamaye ƙasa baki ɗaya.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Yadda lamarin ya faru
Da yake labarta yadda abun ya faru, Muhideen yace:
"Mun halarci shagalin bikin zagayowar ranar haihuwa na ɗaya daga cikin abokan karatun mu ranar Lahadi, muna da yawa waɗanda muka je wurin."
"Ɗaya daga cikinmu ya kwankwaɗi barasa, amma ba dukan mu ne muka sha ba. Lokacin da malamin mu da wasu iyayen mu suka gani tabbas sun fusata."
"Wannan fushin yasa suka mana bulala ranar Laraba, sannan kuma wasun mu sai ranar Asabar suka karbi ta su bulalan."
Shin dagaske ne kun sha barasa?
"Ɗaya daga cikinmu ne ya sha barasa (Trophy), yayin da sauran suka sha Malta Guinness da kuma lemun ƙara kuzari. Wannan ne ainihin abinda ya faru." inji shi.
Sai dai da aka tambayeshi me zai ce game da ɗayan hoton bidiyon da ya nuna yadda sukai wasa da barasa, suka yiwa junansu wanka da ita, ɗalibin yace:
"Bani da masaniya game da wannan, a shagalin da muka halarta ranar Lahadi, babu wanda ya yi wanka da giya. Mutum ɗaya yasa aka kawo masa ita."
Makaranta ta yi dai-dai data hukunta mu
Wani ɗalibin kuma, Abdulmumin Jibrin, wanda yana ɗaya daga cikin ɗaliban da suka sha bulala, ya gode wa hukumar makaranta data hukunta su.
Yace na gargaɗi abokan karatun, waɗanda ba su ji dadin dukan ba, kada su saka bidiyon a kafar sada zumunta, amma suka ƙi jin maganata.
Yace:
"Mun halarci wurin party ranar Lahadi kuma muna da yawa. Uku daga cikinmu sun sha bulala ranar Laraba, yayin da aka bugi sauran ranar Asabar."
"Bayan an bualale mu ranar Laraba, mun san cewa hakan dai-dai ne domin mun cancanci hakan."
2023: Atiku Ya Yi Martani Kan Harin Wasu 'Yan Daba a Wurin Kamfe Ɗinsa a Kaduna, Ya Tura Sako Ga Buhari
"Amma wasu daga cikin mu sun ɗauki bidiyo sun tura kafafe sada zumunta, duk da na faɗa musu kada su yi hakan."
A wani labarin kuma kun ji cewa An dakatar shugaban wata makarantar Larabci da aka ci zarafin wata daliba
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, gwamnatin Kwara ta fara gudanar da bincike kan cin zarafin wata daliba a makarantar Larabci da malamai suka yi.
Gwamnati ta kafa kwamitin bincike, wanda ya kunshi malaman Muslunci, shugabanni da jami’an gwamnati, domin duba lamarin yayin da aka dakatar da shugaban makarantar har sai an kammala bincike.
Asali: Legit.ng