Mustapha Kwankwaso Zai Dauki Matakin Shari'a kan Kwamishinan Abba, Ya ba Shi Zabi

Mustapha Kwankwaso Zai Dauki Matakin Shari'a kan Kwamishinan Abba, Ya ba Shi Zabi

  • Mustapha Rabiu Kwankwaso ya ce zargin cewa an kafa Cibiyar Gyaran Tarbiyya ta Kiru saboda shi ƙarya ne, domin yana Dubai lokacin kafa ta
  • Ya musanta cewa mahaifinsa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, bai amince da shi ba, yana mai cewa ya kafa kamfanoni da kansa
  • Ya ba Kwamishinan Yaɗa Labarai na Kano wa’adin sa’o’i 48 ya janye zargin tare da ba shi haƙuri, ko kuma ya fuskanci matakin shari’a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Mustapha Rabiu Kwankwaso, ɗan tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya musanta zarge-zargen da sabon Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar ya yi masa, yana mai cewa ƙarya ne da nufin ɓata masa suna.

Mustapha, wanda shi ne ɗan takarar mataimakin gwamna a jam’iyyar NDC, ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar domin mayar da martani kan kalaman jami’in gwamnatin jihar.

Kara karanta wannan

Akwai rigima: Gwamna APC da kotu ta kwace takararsa ya sha sabon alwashi

Mustapha Kwankwaso ya yi martani kan zargi Sanusi Bature
Mustapha Rabiu Kwankwaso tare da Sanusi Bature Dawakin Tofa Hoto: Mustapha Rabiu Kwankwaso, Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Dan takarar mataimakin gwamnan na jihar Kano ya sanya sanarwar ne a shafinsa na Facebook a ranar Talata, 10 ga watan Nuwamban 2026.

Ya ce an zarge shi da zuwa cibiyoyin gyaran tarbiyya daban-daban a sassan duniya, tare da cewa shi ne dalilin da ya sa mahaifinsa ya kafa Cibiyar Gyaran Tarbiyya ta Kiru.

Ya musanta alaƙarsa da kafa cibiyar Kiru

Mustapha ya bayyana zargin cewa an kafa cibiyar Kiru ne saboda shi a matsayin ƙarya, yana mai cewa hakan ba zai yiwu ba bisa tarihin lokacin da aka kafa cibiyar.

A cewarsa, a lokacin wa’adin mulki na biyu na mahaifinsa a matsayin gwamnan Kano, lokacin da aka kafa cibiyar, yana can birnin Dubai na ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa.

Ya ce an kafa cibiyar ne a matsayin wata manufa ta gwamnati domin gyara tarbiyyar matasa, taimaka musu su sauya hali da kuma mayar da su cikin al’umma.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya bayyana abin da Tinubu yake tsoro kan zaben 2027

Ya ce mahaifinsa ya amince da shi

Mustapha ya kuma musanta ikirarin cewa mahaifinsa bai taɓa amincewa da shi ya kula da Skyline University, Mewar University ko gonarsa ba.

Ya bayyana hakan a matsayin ƙarya, yana mai cewa mahaifinsa ya horar da shi, ya ba shi tarbiyya kuma ya koyar da shi dogaro da kai.

Ya ce da taimakon Allah, ya kafa sana’o’i da kamfanoni da dama, ciki har da masana’antar sarrafa shinkafa da ke ɗaukar ma’aikata tare da bayar da gudunmawa ga tattalin arzikin Kano.

A cewarsa, ya gina waɗannan sana’o’i ne ta hanyar aiki tuƙuru, jajircewa da tarbiyyar da mahaifinsa ya ba shi, ba ta hanyar dogaro da shi ba.

Ya kare nadin da aka yi masa a matsayin kwamishina

Mustapha ya kuma yi Allah-wadai da yadda kakakin gwamnan ya bayyana naɗin da aka yi masa a matsayin Kwamishinan Matasa da Wasanni da kalmar “gyaran tarbiyya ta hanyar gwamnati”.

Ya gode wa Gwamnan Kano bisa damar da ya ba shi na zama kwamishina da mamba a Majalisar Zartarwa ta Jiha.

Kara karanta wannan

Gwamna ya yi magana mai zafi kan harin da aka kai wa ayarin Peter Obi da Kwankwaso

Ya ce ya yi aikinsa cikin gaskiya, jajircewa da biyayya ga al’ummar Kano, musamman matasa. Ya jaddada cewa ba a naɗa shi kwamishina domin a gyara shi ba, illa domin ya yi wa al’umma hidima, kuma ya yi hakan yadda ya kamata.

Ya ba kwamishinan wa’adin sa’o’i 48

Mustapha ya tambayi sabon Kwamishinan Yaɗa Labarai ko an naɗa shi ne domin sanar da jama’a manufofi, shirye-shirye da nasarorin gwamnati, ko kuma domin ya riƙa kai wa abokan hamayyar siyasa hari.

Ya kuma nemi sanin ko kalaman da ya yi nasa ne ko kuma yana magana ne a madadin gwamnan.

A ƙarshe, Mustapha ya ba kwamishinan wa’adin sa’o’i 48 daga ranar fitar da sanarwar ya janye kalamansa gaba ɗaya, tare da ba shi, iyalinsa da al’ummar Kano haƙuri a bainar jama’a.

Ya gargaɗe shi cewa idan ya ƙi yin hakan, to ya shirya jin ta bakin lauyoyinsa. Mustapha ya ce ba zai bari a ɓata masa suna ko tarihin hidimar da ya yi wa jihar saboda siyasa ba, yana mai cewa ya fi mayar da hankali kan bayar da gudunmawa wajen samar da makoma mai kyau ga Kano.

Ya jaddada cewa siyasa ya kamata ta ta'allaka ne kan manufofi, shirye-shirye da ayyukan da aka gudanar, ba ƙarya da ɓata halayen mutane ba.

Kara karanta wannan

Oshiomhole ya kwance wa Atiku da Peter Obi zani a kasuwa kan zaben 2027

Mustapha Kwankwaso ya yi martani ga Sanusi Bature
Mustapha Rabiu Kwankwaso zaune a ofis Hoto: Mustapha Rabiu Kwankwaso
Source: Facebook

Kwankwaso ya yi zargi kan gwamnatin Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jinkirta karɓar haraji bisa sababbin dokokin haraji.

Sanata Kwankwaso ya yi zargin cewa gwamnatin tarayya ta ɗauki wannan mataki ne saboda fargabar cewa aiwatar da dokokin na iya jawo mata matsala a babban zaɓen 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng