Zaben Shugaban kasa: ‘Dan Atiku Ya Zage da Yi wa Tinubu Kamfe a doke Mahaifinsa a Jigawa

Zaben Shugaban kasa: ‘Dan Atiku Ya Zage da Yi wa Tinubu Kamfe a doke Mahaifinsa a Jigawa

  • Abba Atiku ya jagoranci ƙungiyarsa ta Haske zuwa Jigawa, kuma ya narkar da ita cikin APC domin goyon bayan Bola Tinubu.
  • Ƙungiyar ta ce za ta mara wa shugaban Najeriya baya a zaɓen 2027 domin ya kammala wa'adin shekaru takwas a kan karagar mulki
  • Gwamnan Jigawa, Umar Namadi, ya yabi aikin Abba, ya yi alƙawarin haɗa kai da ƙungiyar domin ganin APC ta yi galaba a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Jigawa - Abba Atiku, ɗan tsohon mataimakin shugaban ƙasar Najeriya ya jagoranci tawagar wata ƙungiyarsa ta siyasa zuwa jihar Jigawa.

Abba Atiku Abubakar da mutanensa sun je Jigawa domin bayyana goyon bayansu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu gabanin ziyarar da zai kai.

Abba Atiku da Tinubu
Abba Atiku da kuma Shugaban kasa Bola Tinubu da mai dakinsa ana kamfe Hoto: Bayo Onanuga/Imran Muhammad
Source: Facebook

Mutanen Abba Atiku sun tafi jihar Jigawa

Abba Atiku, wanda ya kafa ƙungiyar Haske, ya sanar da cewa ƙungiyar ta haɗa mutanenta sun tafi Jigawa kamar yadda Premium Times ta fada.

Kara karanta wannan

Okowa: Abokin takarar Atiku a 2023 ya bayyana dalilin da ya sa suka raba gari ya koma APC

Ƙungiyar ta kuma narke cikin jam’iyyar APC mai mulki domin ta mara wa Bola Tinubu baya a ƙoƙarinsa na neman wa'adi na biyu a zaɓen 2027.

Matashin ya bayyana cewa sun ɗauki wannan mataki ne domin ganin Tinubu wanda ya fito daga yankin Kudu ya kammala wa'adin shekaru takwas.

Darakta-Janar na ƙungiyar Haske Bola Ahmed Tinubu Organisation, ya ce tafiyar da aka kafa a shekarar 2019 domin tallar Atiku ta canza akala.

Usman Meyari yake cewa yanzu Haske ta yanke shawarar mara wa Tinubu baya ya zarce a ofis.

Meyasa Abba Atiku suka bi Bola Tinubu?

An rahoto Meyari a ranar Litinin yana mai bayyana cewa matasa na goyon bayan Tinubu ne domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankalin ƙasa.

Ya ce bai kamata Arewa ta matsa wajen karɓar mulki tun kafin duka wa'adin shugaban ya cika ba, suna ganin kyau a bar mutanen Kudu su shekara takwas.

Kara karanta wannan

Sanata Yari ya yi wa yankin Tinubu gori kan kuri'u, ya bugi kirki kan Arewa

Yanzu haka ana da labari cewa mutane sun cika ana jiran jirgin shugaban kasa ya isa Jigawa, saboda haka ne gwamnatin jihar ta ce babu aiki a yau/

Gwamnan jihar Jigawa ya jinjina wa Abba Atiku

A nasa jawabin, Gwamnan Jigawa, Umar Namadi, ya yaba wa ƙungiyar bisa matakin da ta ɗauka, tare da tabbatar musu da cikakken goyon bayansa.

Mai girma Gwamnan ya ce jam'iyyar APC a Jigawa za ta yi aiki tare da ƙungiyar domin ganin Tinubu ya samu gagarumin rinjaye a jihar a zaɓe mai zuwa.

Yaron Atiku yana yakar shi daga gida

Rahoto ya zo cewa Abba Atiku, wanda ɗan tsohon mataimakin shugaban ƙasa ne ya jagoranci tawagarsa zuwa jam'iyyar APC domin goyon bayan tazarcen Bola Tinubu.

Ya bayyana cewa kungiyarsa ta 'Haske' ta koma APC ne saboda goyon bayan a zagaya da mulki tsakanin Arewa da Kudu da kuma ganin irin kokarin da APC take yi.

A cewarsa, babu wani mutum ko jam'iyyar da za ta hana Tinubu lashe zaɓen 2027 ba, inda ya nuna cewa za su yi aiki tuƙuru domin ganin shugaban ya samu nasara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng