Halin da yan bindiga suke jefa mutane tun bayan katse hanyoyin sadarwa a jihar Katsina

Halin da yan bindiga suke jefa mutane tun bayan katse hanyoyin sadarwa a jihar Katsina

  • Duk da matakan da gwamnatin jihar Katsina ta ɗauka, mazauna jihar sun fara kokawa kan yawaitar ayyukan yan bindiga
  • A cewar mazauna ƙaramar hukumar Faskari, yan bindiga na cigaba da cin karensu babu babbaka
  • Mutanen sun yaba da kokarin jami'an tsaro amma suna ganin rashin sabis na hana su neman kawo ɗauki

Katsina - Mutanen ƙaramar hukumar Faskari a jihar Katsina sun koka kan yadda yan fashi suka cigaba da aikata ta'addancinsu duk da ƙoƙarin sojoji da matakan da gwamnati ta ɗauka.

Premium times ta rahoto cewa wannan na zuwa ne bayan gwamnatin jihar ta yi ikirarin cewa matakan da ta ɗauka sun fara haifar da ɗa mai ido.

Ƙungiyoyi da kuma ɗai-ɗaikun mutane musamman a ƙaramar hukumar Faskari sun fara ƙorafin cewa yan bindiga na musu kisan mummuƙe a ƙauyukansu.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ne ɗan siyasan da yafi kowane farin jini da Nagarta a wannan zamanin, Osinbajo

Jihar Kastina
Halin da yan bindiga suke jefa mutane tun bayan katse hanyoyin sadarwa a jihar Katsina Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Yan fashi na kashe mu a sirrince - muatane

A wani jawabi da ta aike ofishin gwamnan jiha, ƙungiyar cigaban yankin Daudawa, ta bayyana cewa matakan da gwamnati ta ɗauka ya shafi mutane fiye da yan bindigan.

Shugaban ƙungiyar, Hassan Usman, yace a halin yanzun yan bindiga suna kawo hari da sanin cewa mutane ba su da hanyar da zasu usar da bayanai ga jami'an tsaro.

Yace:

"Mun shiga wani yanayi na rashin tsaro mafi muni yanzu, domin mahara suna shirya kansu su kawo mana hari da kwarin guiwarsu."
"Saboda sun san bamu da hanyar isar da bayanai, ba mu da hanyar neman ƙarin jami'an tsaro."

Duk da cewa ya yaba da jami'an tsaron masu aiki a yankin, amma yace suna fuskantar ƙalubale wajen neman a kawo ɗauki.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Jami'an Kwastam sun sake bude wuta kan jama'a a jihar Katsina

Mutane sun gudu

Mutane sun bayyana cewa yawaitar hare-haren da yan bindiga ke kaiwa Daudawa ya tilastawa mazauna garin da dama gudun hijira.

Rahoto ya tabbatar da cewa a Daudawa kaɗai, yan bindiga sun hallaka mutum 9, sannan kuma suka yi awon gaba da wasu, bayan ƙone gidaje da motoci.

Ta ya zamu bada rahoton an kawo mana hari?

Wani ɗan garin Daudawa, Lawal Ibrahim, ya yi kira ga gwamnati ta sassauta matakin datse sadarwa saboda mutane su samu damar bada rahoton hari.

Yace:

"Lokacin da suka kawo hari Daudawa ranar Lahadi, sun faɗa mana cewa shirinsu na gaba shine zasu kai hari Unguwar Samanja, babu nisa daga nan."

Shin gwamnati tasan halin da mutane ke ciki?

Mai baiwa gwamna Aminu Bello Masari shawara ta musamman kan harkokin tsaro, yace gwamnati bata ɗauki waɗannan matakan domin ta takura wa al'ummarta ba.

Ya kara da cewa gwamnati na nazari a kan tasirin matakan, kuma zata ɗauki matakin da ya dace bisa duk abinda ta gano.

Kara karanta wannan

Yan sakai sun hallaka limamin masallaci da wasu mutum 10 a jihar Sokoto

A wani labari na daban mun tattaro muku Yadda mata ke amfani da Hijabi wajen safarar muggan makamai ga yan fashi a Najeriya

Wasu mata biyu da jami'an yan sanda suka cafke sun bayyana yadda suke tallafawa yan fashi ta hanyar amfani da Hijabi.

Matan sun bayyana yadda suke ɗaukar bindigu AK-47 daga wani wuri a umarce su kai ta wani wuri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262