Da dumi-dumi: Majalisar tarayya za ta zartar da kasafin kudin 2022 kafin karshen shekarar 2021 - Lawan

Da dumi-dumi: Majalisar tarayya za ta zartar da kasafin kudin 2022 kafin karshen shekarar 2021 - Lawan

  • Sanata Ahmad Lawan, shugaban majalisar dattawa, ya bayyana cewa majalisar dokokin kasar za ta zartar da kasafin kudin shekarar 2022 kafin karshen 2021
  • Shugaban majalisar ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a taron gabatar da kasafin kudin da Shugaba Buhari yayi a gaban majalsar hadin gwiwa
  • Ya kuma ce za gabatar da kudirin kudin kafin karshen shekarar domin bayar da damar kula da sabon tsarin kasafin kudin

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya ce majalisar dokokin tarayya ta kuduri aniyar zartar da kasafin kudin shekarar 2022 kafin karshen wannan shekarar.

Da dumi-dumi: Majalisar tarayya za ta zartar da kasafin kudin 2022 kafin karshen shekarar 2021 - Lawan
Da dumi-dumi: Majalisar tarayya za ta zartar da kasafin kudin 2022 kafin karshen shekarar 2021 - Lawan Hoto: Vanguard
Source: Facebook

Lawan, a cikin jawabinsa a wurin taron gabatar da kasafin kudin, ya tuno da yadda Majalisar Tarayya ta 9 ta yi alkawarin dawo da Najeriya cikin tsarin kasafin kudi na Janairu zuwa Disamba da kasafin kudin 2020 kuma hakan ya yiwu.

Read also

Za ka iya karban bashi don aiwatar da Kasafin Kudin 2022, Shugaban Majalisa ga Buhari

Ya kara da cewa an maimaita irin wannan bajintar da kasafin kudin 2021 kamar yadda jaridar Punch ta rahoto.

Yayin da yake godiya ga Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, kan gabatar da kasafin kudi da wuri, Shugaban Majalisar Dattawan ya ce 'yan majalisar za su gabatar da kudirin kudin kafin karshen shekarar 2021.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahoton ya kuma kawo cewa Lawan ya ce za a yi hakan ne domin bayar da damar kula da sabon tsarin kasafin kudin.

Shugaba Buhari ya dira majalisar dokokin tarayya domin gabatar da kasafin kudin 2022

A gefe guda, mun ji cewa da misalin karfe 12:06, Shugaba Muhammadu Buhari ya isa majalisar dokokin tarayya domin gabatar da kasafin kudin 2022.

Buhari ya samu rakiyan manyan ministoci da hadimansa.

Shugaban majalisar dattawa ya bukaci Sanata Opeyemi Bamidele ya bude taron da addu'a Kirista, yayinda Dan majalisa El-Makky Liman zai yi addu'an Musulmai.

Read also

Muhimman Abubuwa 10 da Shugaba Buhari ya fada a jawabinsa ga yan majalisa ranar Alhamis

An tsaurara tsaro yayinda Shugaba Buhari ke shirin gabatar da kasafin kudin 2022 yau

Mun kuma kawo a baya cewa Shugaba Muhammadu Buhari zai gabatar da daftarin kasafin kudin shekarar 2022 ga hadin gwiwar majalisar dokokin kasar a ranar Alhamis.

Mataimakin shugaban majalisar dattijai, Ovie Omo-Agege ne ya bayyana hakan a ranar Talata 5 ga watan Oktoba a zauren majalisar dattawa da ke Abuja.

Ya sanar da hakan ne yayin da yake jagorantar zaman majalisar yayin da shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, bai halarci taron ba.

Source: Legit

Online view pixel