KAI TSAYE: Yadda gabatar da kasafin kudin 2022 da Shugaba Buhari keyi ke gudana

KAI TSAYE: Yadda gabatar da kasafin kudin 2022 da Shugaba Buhari keyi ke gudana

Komai ya kankama domin gabatar da kasafin kudin 2022 a gaban yan majalisar wakilai da na dattawa a hade. Ana sa ran zai isa majalisar misalin karfe 11 na safe.

Yan majalisar dattawa sun katse zamansu da sukeyi yanzu haka domin garzayawa zauren majalisar wakilai inda Shugaba Buhari zai same su.

Shugaban masu rinjaye na majalisar, Sanata Yahaya Abdullahi da Shugaban marasa rinjaye Eyinayya Abaribe, ne suka mika bukatar hakan.

Buhari ya kammala jawabinsa kuma ya gabatar da kasafin kudin gaban yan majalisa

Shugaba Muhammadu Buhari ya kammala jawabinsa a kuma ya gabatar da kasafin kudin N16tr.

Yanzu yana shirin fita daga cikin majalisar.

An gayyaci Buhari, ya fara gabatar da jawabinsa

Shugaba Buhari ya ce:

"Ina godiya gareku yan majalisa bisa kaimin da kuka yi wajen amincewa da MTEF."
"Ba zai tsawaita magana ba yanzu, zan dan yi wasu bayanai sama-sama daga baya Ministar kudi ta yi bayani dallda-dalla."
Zaku tuna cewa a baya mun ce zamu daina biyan tallafin mai mu bari yanz kasuwa su rika zaben farashin, amma da muka ga litan mai ya fara kai wa N155, sai muka ga abin ba zai yiwu ba"
Shi yasa muka cigaba da biyan tallafin mai kuma wannan ya shafi ayyukan da mukayi niyyar yi da kudi."
Duk da rashin kudi, muna biyan kowa albashinsa kuma ko a ranar 1 ga Oktoba, mun saki N1.73tr don wasu manyan ayyuka.
Mun samu nasarori wajen gina layin dogon jiragen kasa irinsu na Legas-Ibadan, Kaduna-Abuja, kuma na an Itakpe-Warri bayan shekaru 30 da farawa.
An shirya kammala Ibadan-Kano, Calabar-Legas wanda ya hada kudu da Arewa."
Muna cigaba da kokarin kammala titunan Legas-Ibadan, Abuja-Kano, EastWest kafin wa'adinmu ya kare a 2023."

Bayanai kan kasafin kudin 2022

Mun yi wa wannan kasafin kudi take "kasafin kudin samar da cigaban ga al'umma

Mun yi kiyasin wannan kasafin kudin bisa wadannan abubuwa:

1. Farashin danyan mai – $57 ga ganga

2. Za'a rika hakan gangan danyan mai milyan 1.88 kulli yaumin

3. Farashin Dala - N410.15/US$;

4. Kudin shiga na mai N3.16 trillion

5. Kudin shiga na haraji – N2.13 trillion.

6. GDP 4.2%

Kudin da muke sa ran kashewa a 2022 - 16.39tr

Kudin albashi - N6.8tr

Fansho, gratuti - N577bn

Manyan ayyuka - N5.35tr

Kudin Bashin da zamu biya - N3.61tr

Kudin da zamu nema nan gaba don aiwatar da kasafin kudin - N6.22tr

Zamu ciyo bashin - N5.01tr

"Wasu suna maganganu kan basussukan da muke karba, hakane, amma basussukan da muke karba ba suyi yawa ba tukun, har yanzu muna kan hanya."

"Mun yi amfani da wadannan basususkan wajen ayyukan alfanu ga al'ummanmu"

Mun kashesu wajen:

- Kammala ayykan hanyoyi da layin dogo

- Wutan lantarki

- Ruwan sha

- Ayyukan asibiti da kiwon lafiya (Sayan rigakfin korona, dss)

Shugaban majalisar dattawa ya fara jawabin bude taronsa

Yace:

"Yan Najeriya na amfana da saurin kaddamar da kasafin kudin 2021."
"Wannan ya taimakawa wannan kasar wajen samun cigaba duk da annobar COVID-19"
"Karban haraji har yanzu babban matsala ne ga kasarmu. Majalisar dokoki ta dauki matakai wajen ganin ma'aikatun gwamnati na samar da kudin shiga."
"Mun fahimci cewa ya wajibi gwamnatin nan ta karbi bassusuka don yin ayyukansa shi yasa muke amincewa, amma duk da haka ya kamata mu samar da wata hanyar samun kudi."
"Ina yawa maka (Shugaba Buhari) na fara aiwatar da dokar PIA)

Shugaba Buhari ya dira majalisar dokokin tarayya

Misalin karfe 12:06, Shugaba Muhammadu Buhari ya isa majalisar dokokin tarayya domin gabatar da kasafin kudin 2022.

Buhari ya samu rakiyan manyan ministoci da hadimansa.

Shugaban majalisar dattawa ya bukaci Sanata Opeyemi Bamidele ya bude taron da addu'a Kirista, yayinda Dan majalisa El-Makky Liman zai yi addu'an Musulmai

A wannan lokaci

Shugaban majalisar dattawa tare da sauran sanatocin Najeriya sun isa majalisar wakilai.

Yanzu Shugaba Muhammadu Buhari ake sauraro

Online view pixel