Za ka iya karban bashi don aiwatar da Kasafin Kudin 2022, Shugaban Majalisa ga Buhari

Za ka iya karban bashi don aiwatar da Kasafin Kudin 2022, Shugaban Majalisa ga Buhari

  • Shugaban majalisa ya ce karban bashi ya zama dole idan ana son gwamnati tayi aiki
  • Ahmad Lawan yace dalilin da yasa majalisa ke amincewa Buhari ya karba kenan
  • Masana sun ce wannan basussuka na iya zama matsala ga Najeriya

Abuja - Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari zai iya cigaba da karban basussuka saboda Najeriya na bukatar kudi yanzu.

A cewarsa, wannan shine dalilin da yasa suke amincewa duk lokacin da Shugaban kasan ya nemi izinin karban bashi.

Ahmad Lawan ya yi wannan jawabi ne lokacin da Shugaban kasa ya tafi majalisar gabatar da kasafin kudin 2022.

Yace:

"Mai girma Shugaban kasa, samar da kudin shiga har yanzu babban kalubale ne ga cigaban da muke so.

Kara karanta wannan

Buhari ya yi alkawari Gwamnatinsa za ta kammala ayyukan da ta fara kafin ya bar mulki

"Shi yasa kwanan nan majalisa da bangaren zartaswa suka yanke shawaran a daina baiwa ma'aikatun da suke kin shigar da kudin shigan 2022 wasu kudade."
"Ya kai Shugaban kasa, mun fahimci cewa sakamakon rashin kudi, ya zama wajibi gwamnati ta karbi basussuka daga gida da kasashen waje domin gudanar da ayyuka a fadin tarayya."
"Shi yasa muke bada daman karban wadannan basussuka. Wajibi ne a cika alkawuran da aka yiwa mutane saboda haka sai an samo kudi ta ko wani hanya."

Za ka iya karban bashi don aiwatar da Kasafin Kudin 2022, Shugaban Majalisa ga Buhari
Za ka iya karban bashi don aiwatar da Kasafin Kudin 2022, Shugaban Majalisa ga Buhari Hoto: Tolani Alli
Asali: Facebook

Masana sun yi gargadi ga basussukan da ake karba

Tsokaci kan kasafin kudin, shugaban cibiyar cigaban yan kasuwa masu zaman kansu, Dr Muda Yusuf, yace kasafin kudin 2022 na N16.39trillion ya fi na 2021 yawa na rubu'i (N13.08 trillion).

Yace:

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Gwamnatin Buhari ta ware biliyoyin Nairori ga likitoci, ladan dage yajin aiki

"Biyan bashi zai cigaba da zama matsala da nauyi ga kudin gwamnati, kuma CBN za ta cigaba da samun matsalan kudi. Wannan na da illa sosai saboda zai haifar da hauhawan kaya."

Ya kara da cewa gaba daya kudaden da za'ayi manyan ayyuka da su bashinsu za'a ci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel