An tsaurara tsaro yayinda Shugaba Buhari ke shirin gabatar da kasafin kudin 2022 yau

An tsaurara tsaro yayinda Shugaba Buhari ke shirin gabatar da kasafin kudin 2022 yau

  • Majalisar dattawa ta shirya tsaf don karban bakuncin Shugaba Muhammadu Buhari
  • An tsaurara tsaro yanzu haka a Majalisar dokokin tarayya
  • Buhari zai gabatar da Kasafin Kudin 2022 na N16.39tr yau

Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari zai gabatar da daftarin kasafin kudin shekarar 2022 ga hadin gwiwar majalisar dokokin kasar a ranar Alhamis.

Mataimakin shugaban majalisar dattijai, Ovie Omo-Agege ne ya bayyana hakan a ranar Talata 5 ga watan Oktoba a zauren majalisar dattawa da ke Abuja.

Ya sanar da hakan ne yayin da yake jagorantar zaman majalisar yayin da shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, bai halarci taron ba.

Shugaba Buhari zai gabatar da kasafin kudin 2022 yau, za'a kashe N16.39tr
Shugaba Buhari zai gabatar da kasafin kudin 2022 yau, za'a kashe N16.39tr Hoto: Presidency
Source: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Read also

An tattauna da 'yan bindiga a Zamfara, sun sako mutane sama da 200

A cikin wasikar da ya aike wa Majalisar Dattawa, Shugaban ya bukaci ‘yan majalisar su amince da takardun tsare-tsare wadanda ya ce za su zama ginshiki da hasashe a cikin kasafin kudin na 2022.

Ya bayyana cewa gyare-gyare sun nuna sabbin sharuddan kasafin kudi a cikin Dokar Masana'antar Man Fetur da aka sanya a kwanan nan, da kuma Dokar Kasafi ta 2022.

Wannan gyaran, a cewar Shugaba Buhari, zai nuna kudaden da za a bai wa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) don shirya babban zaben 2023.

Abubuwan da kasafin kudin zai dogara kai

Ministar kudin tarayya ta bayyana wasu abubuwan da Buhari zai fadawa yan majalisa idan ya bayyana gabansu yau.

A cewarta abubuwan zasu dogara kan

1. Farashin danyan mai – $57 ga ganga

2. Za'a rika hakan gangan danyan mai milyan 1.88 kulli yaumin

3. Farashin Dala - N410.15/US$;

Read also

Yanzu Yanzu: Na kai karar Malami gaban Buhari, kuma bai amince da dokar ta-baci ba a Anambra - Gwamna Obiano

4. Kudin shiga na mai N3.15 trillion

5. Kudin shiga na haraji – N2.13 trillion.

Source: Legit

Online view pixel