Muhimman Abubuwa 10 da Shugaba Buhari ya fada a jawabinsa ga yan majalisa ranar Alhamis
Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Alhamis, 7 ga watan Satumba, 2021 ya gabatar da kasafin kudin 2022 gaban mambobin majalisar dokokin tarayya.
Shugaban kasan ya yi jawabin kimanin mintuna 30 inda ya bayyana abubuwan da gwamnatinsa tayi da kasafin kudin 2021 da kuma abubuwan da yake niyyar yi da kasafin kudin 2022.
Ya bayyana adadin kudaden da za'a kashe kan albashi da manyan ayyuka na musamman.
Legit ta tattaro muku muhimman abubuwa 10 da shugaban kasan ya fadi
1.
Zaku tuna cewa a baya mun ce zamu daina biyan tallafin mai mu bari yanz kasuwa su rika zaben farashin, amma da muka ga litan mai ya fara kai wa N155, sai muka ga abin ba zai yiwu ba"
Shi yasa muka cigaba da biyan tallafin mai kuma wannan ya shafi ayyukan da mukayi niyyar yi da kudi."
2.
Duk da rashin kudi, muna biyan kowa albashinsa kuma ko a ranar 1 ga Oktoba, mun saki N1.73tr don wasu manyan ayyuka.
3.
"Mun samu nasarori wajen gina layin dogon jiragen kasa irinsu na Legas-Ibadan, Kaduna-Abuja, kuma da Itakpe-Warri bayan shekaru 30 da farawa.
An shirya kammala Ibadan-Kano, Calabar-Legas wanda ya hada kudu da Arewa."
4.
Muna cigaba da kokarin kammala titunan Legas-Ibadan, Abuja-Kano, EastWest kafin wa'adinmu ya kare a 2023."
5.
Mun yi wa kasafin kudin 2022 taken "kasafin kudin samar da cigaba ga al'umma"
6.
"Zamu ciyo bashin - N5.01tr"
7.
"Wasu suna maganganu kan basussukan da muke karba, hakane, amma basussukan da muke karba ba suyi yawa ba tukun, har yanzu muna kan hanya."
8. "Mun yi amfani da wadannan basususkan wajen ayyukan alfanu ga al'ummanmu"
Mun kashesu wajen:
- Kammala ayykan hanyoyi da layin dogo
- Wutan lantarki
- Ruwan sha
- Ayyukan asibiti da kiwon lafiya (Sayan rigakafin korona, dss)
9. Mun yi kiyasin wannan kasafin kudin bisa wadannan abubuwa:
1. Farashin danyan mai – $57 ga ganga
2. Za'a rika hakan gangan danyan mai milyan 1.88 kulli yaumin
3. Farashin Dala - N410.15/US$;
4. Kudin shiga na mai N3.16 trillion
5. Kudin shiga na haraji – N2.13 trillion.
6. GDP 4.2%
10. Kudin da muke sa ran kashewa a 2022 - 16.39tr
Kudin albashi - N6.8tr
Fansho, gratuti - N577bn
Manyan ayyuka - N5.35tr
Kudin Bashin da zamu biya - N3.61tr
Kudin da zamu nema nan gaba don aiwatar da kasafin kudin - N6.22tr
Asali: Legit.ng