Dalilin da yasa na kira Tinubu 'Shugaban kasa' a kasar waje - Dan majalisa yayi bayani kan bidiyon da ya bazu

Dalilin da yasa na kira Tinubu 'Shugaban kasa' a kasar waje - Dan majalisa yayi bayani kan bidiyon da ya bazu

  • Abubakar Lado Suleja, dan majalisar wakilai daga jihar Neja ya yi martani a kan wani bidiyo wanda a ciki ya kira Asiwaju Bola Tinubu, a matsayin ‘Mai girma Shugaban kasa’
  • Lado ya bayyana cewa ya kira Tinubu da 'shugaban kasa' ne saboda shi suke fatan ya gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari
  • Ya kuma musanta ikirarin cewa ziyarar da suka kai ma jigon na APC yana nufin lamunce masa a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar

Wani dan majalisar wakilai, Abubakar Lado Suleja (APC, Niger) ya yi bayanin bidiyon da ya shahara, wanda a ciki ya kira Asiwaju Bola Tinubu, a matsayin ‘Mai girma Shugaban kasa’ a lokacin da suka ziyarce shi a Landan a makon da ya gabata.

Shugabannin kungiyoyin Arewa na APC, karkashin jagorancin mataimakin kakakin majalisar, Ahmed Wase, sun ziyarci Tinubu a Landan a ranar 1 ga watan Oktoba.

Read also

Jerin yan arewa da Tinubu zai iya dauka a matsayin abokan takara idan ya shiga tseren shugaban kasa na 2023

Dalilin da yasa na kira Tinubu 'Shugaban kasa' a kasar waje - Dan majalisa yayi bayani kan bidiyon da ya bazu
Dalilin da yasa na kira Tinubu 'Shugaban kasa' a kasar waje - Dan majalisa yayi bayani kan bidiyon da ya bazu Hoto: Daily Trust
Source: UGC

A cikin bidiyon, Suleja ya cewa Tinubu yayin da ya yi kokarin shiga motarsa: "Mai girma Shugaban kasa, sai anjima." Tinubu ya amsa da "Na gode."

Suleja ya tabbatar wa jaridar Daily Trust cewa ya kira Tinubu a matsayin Shugaban kasa.

Lokacin da aka tambaye shi ko yanzu kasar tana da shugabannin kasa biyu ne, sai ya ce:

“A’a, ba mu da shugabanni biyu, watakila ba ku saurari bidiyon sosai ba saboda lokacin da na ce Shugaban kasa, Insha Allah ya biyo baya, wanda ke nufin da yardar Allah.
"Muna yi masa addu’an zama shugaban Najeriya na gaba. Muna da shugaban kasa daya tilo wanda shine Shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda shine jagoran jam’iyyarmu kuma mai ba mu shawara amma muna addu’ar Asiwaju ya zama shugaban Tarayyar Najeriya na gaba kuma ya ci gaba daga inda shugaba Buhari zai tsaya. Abin da nake nufi kenan.

Read also

Ba ma son Biyafara, kawai muna so ayi mana adalci daidai da kowa ne - Gwamna Umahi

“Manufar ziyarar mu ita ce ganin yanayin lafiyarsa, yi masa addu’a da fatan alheri. Yana cikin koshin lafiya kuma kamar yadda kuke gani daga bidiyon, yana cikin yanayi mai kyau. Ya kusan awa daya yana yi mana magana.”

Suleja ya musanta ikirarin cewa ziyarar tasu ita ce ta amince da takarar Tinubu a matsayin shugaban kasa, PM News ta kuma ruwaito.

"A'a, ziyarar ba don lamunce masa bane, mu masu biyayya ne, masoya kuma shi ne jagoranmu. Idan mutane na cewa don amince masa ne, to hakan na nufin Shugaba Buhari ya amince da shi saboda Shugaba Buhari ne ya fara ziyartar shi.”

Ina cikin koshin lafiya, kawai na duba lafiya na ne, Asiwaju Bola Tinubu

A baya mun kawo cewa babban jigon jam'iyyar All Progressives Congress APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya bayyana cewa yana cikin koshin lafiya kawai dai ana cigaba da duba lafiyarsa ne a Landan.

Read also

Babbar Magana: Sanata na goyon bayan IPOB, ya ce akwai kungiyoyin aware a kudu sun fi 30

Tinubu ya bayyana hakan ne yayin jawabi ga yan Arewa mambobin majalisar wakilan tarayya da suka kai masa ziyara ranar Juma'a.

Tinubu, wanda tsohon gwamnan Legas ne ya kwashe watanni uku yanzu a birni Landan tun bayan da aka yi masa aikin tiyata a gwiwa.

Source: Legit

Online view pixel