Babbar Magana: Sanata na goyon bayan IPOB, ya ce akwai kungiyoyin aware a kudu sun fi 30

Babbar Magana: Sanata na goyon bayan IPOB, ya ce akwai kungiyoyin aware a kudu sun fi 30

  • Santa daga yankin kudu maso gabas ya bayyana goyon bayansa ga kungiyar ta'addanci ta IPOB
  • Sanatan ya ce, akalla akwai kungiyoyi sama da 30 da ke fafutukar ballewa daga Najeriya a yankin
  • Ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa a wata hira a gidan talabijin na Channels jiya Talata

Shugaban marasa rinjaye na majalisar dattijai, Enyinnaya Abaribe, ya ce akwai sama da kungiyoyin ‘yan aware 30 a yankin Kudu maso Gabas da ke da zimmar aiwatar da burinsu na kafa Biafra.

Abaribe, a wata hira da aka yi da shi a ranar Talatar da ta gabata a gidan Talabijin na Channels, ya yi zargin cewa ana kuntatawa mutanen yankin kuma ana yi musu rashin adalci.

Babbar Magana: Sanata na goyon bayan IPOB, ya ce akwai kungiyoyin aware a kudu sun fi 30
Sanata Enyinnaya Abaribe | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Legit.ng Hausa ta rahoto daga Daily Trust inda Abaribe ke cewa:

“Babbar matsalar da kafafen watsa labarai ma ke da ita ita ce danganta komai da ya faru da kungiyar IPOB yankin Kudu maso Gabas.
"Ba za ku yi imani cewa akwai kungiyoyi daban-daban na 'yan aware sama da 30 ba. IPOB, MASSOB, suna da yawa kuma kowanne daga cikinsu yana tafiya akan abu guda ne.
"Dalilin da yasa muke tayar da zaune tsaye a ko'ina a cikin kasar shine cewa wasu mutane basa iya gane bambancin mu."

Ya ce gwamnatin yanzu za ta iya murkushe kungiyoyin 'yan aware a shiyyar, amma ba za ta iya kashe akidar ba idan ba a magance musabbabin tashin hankalin ba.

Ina goyon bayan mutane, ciki har da IPOB, inji Abaribe

Da aka tambaye shi ko shi mai goyon bayan IPOB ne, Abaribe ya ce:

"Ni mai goyon bayan koken mutanenmu ne kan rashin adalci ... ina tare da mutanena."

Ya ce bai yi nadamar tsayawa a matsayi daya daga cikin wadanda za su tsaya wa jagoran IPOB, Nnamdi Kanu a shekarar 2017 ba.

'Yan ta'addan IPOB sun kona gidan hadimin gwamnan jihar Legas

A wani labarin mai kama da wannan, wasu tsageru da ba a san ko su waye ba sun kai hari gidan Joe Igbokwe, mai taimakawa gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, a Nnewi, jihar Anambra.

Hakazalika an kona gidan jigon na jam'iyyar APC a ranar Lahadi da yamma, 3 ga watan Oktoba, inji rahoton Sahara Reporters.

Igbokwe wanda ke zaune a jihar Legas ya zargi 'yan ta'adda masu fafutukar a ware na kafa kasar Biafra wato IPOB da alhakin kai harin.

A cikin wani sakon da ya wallafa a Facebook, ya lura cewa kyamarorin CCTV sun nadi kone-kone yayin da suke isa cikin abin hawa a gidansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel