Ina cikin koshin lafiya, kawai na duba lafiya na ne, Asiwaju Bola Tinubu

Ina cikin koshin lafiya, kawai na duba lafiya na ne, Asiwaju Bola Tinubu

  • Watanni uku yanzu, babban jagoran APC na cigaba da jinya a birnin Landa
  • Akalla manyan yan siyasa 40 sun yi tattaki daga Najeriya zuwa can don gaishe da shi
  • Ana sa ran Tinubu zai yi takaran kujeran shugaban kasa a 2023

London - Babban jigon jam'iyyar All Progressives Congress APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya bayyana cewa yana cikin koshin lafiya kawai dai ana cigaba da duba lafiyarsa ne a Landan.

Tinubu ya bayyana hakan ne yayin jawabi ga yan Arewa mambobin majalisar wakilan tarayya da suka kai masa ziyara ranar Juma'a.

Tinubu, wanda tsohon gwamnan Legas ne ya kwashe watanni uku yanzu a birni Landan tun bayan da aka yi masa aikin tiyata a gwiwa.

Amma yanzu yace kawai yana hutawa ne duba lafiyarsa lokaci bayan lokaci ne matsalan, rahoton Punch.

Read also

Rahoto: Yadda Bagudu ya wawuri biliyoyi tare da boyesu a ketare tun zamanin Abacha

A jawabin da yayi musu yana mai sanye da Kaftani da jar hula, Tinubu yace:

"Saboda Allah sannan mutane irinku, ina cikin koshin lafiya. Kawai duba lafiyar ne yayi tsanani."

Ina cikin koshin lafiya, kawai na duba lafiya na ne, Asiwaju Bola Tinubu
Ina cikin koshin lafiya, kawai na duba lafiya na ne, Asiwaju Bola Tinubu
Source: Facebook

'Yan majalisar wakilan arewa sun kai ziyarar wa Tinubu birnin London

Yan majalisar wakilan Najeriya na arewacin kasar nan sun samu jagorancin mataimakin kakakin majalisa, Ahmed Idris Wase inda suka ziyarci jigon jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu a London ranar cikar Najeriya shekaru sittin da daya da samun 'yancin kai.

'Yan majalisar wakilan sun hada da na yankin arewa maso gabas, arewa maso yamma da arewa ta tsakiya.

Source: Legit.ng

Online view pixel