Ba ma son Biyafara, kawai muna so ayi mana adalci daidai da kowa ne - Gwamna Umahi

Ba ma son Biyafara, kawai muna so ayi mana adalci daidai da kowa ne - Gwamna Umahi

  • Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi ya bayyana fafutukar Biyafara a matsayin hauka, yana mai cewa mafi yawan masu fada aji a yankin ba sa son shi
  • Umahi ya ce abu daya da suke so ayi masu shine ayi masu adalci daidai da kowa a kasar
  • Ya kuma bayyana cewa mutanen kudu maso gabas suna yin biyayya ga umurnin zaman gidan ne kawai don tsoro ba wai don suna son yin biyayya ba

Gwamnan jihar Ebonyi, wanda kuma shine Shugaban Kungiyar Gwamnonin Kudu maso Gabas, David Umahi, ya bayyana fafutukar Biyafara a matsayin hauka, yana mai cewa mafi yawan masu fada aji a yankin ba sa son shi.

A cewarsa, kaawai abun da duk suke so shi ne a kula da su daidai da sauran yankunan kasar nan.

Kara karanta wannan

2023: Jigon APC da ya shiga gidan yari ya fito, yana maganar neman Shugaban kasa

Ba ma son Biyafara, kawai muna so ayi mana adalci daidai da kowa ne - Gwamna Umahi
Ba ma son Biyafara, kawai muna so ayi mana adalci daidai da kowa ne - Gwamna Umahi Hoto: David Umahi
Asali: UGC

Gwamna Umahi ya fadi haka ne a ranar Laraba, 6 ga watan Oktoba, yayin da ya bayyana a shirin Sunrise Daily na gidan Talabijin na Channels.

Ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Duk wani fitacce a yankin kudu maso gabas baya son Biyafara. Ba ma son Biyafara. Muna son kawai a kula da mu daidai da sauran yankuna a Najeriya.”
"Don haka, wannan tunanin Biyafara, Biyafara hauka ne".

Ya yi tir da tabararewar abin da ya fara a matsayin kukan adawa da nuna wariya zuwa tashin hankali a yankin, yana mai cewa:

"Ba za ku taba iya fitar da wata kasa daga cikin kasa ba ta irin maganganun ƙiyayya da ake watsawa sannan daga maganganun ƙiyayya zuwa barazanar kashe-kashe da kafa kungiyoyin yan bindiga.
“Idan kuna fada don kare mu to me yasa kuke kashe mu? Mu ne muke kashe kanmu. Lokaci-lokaci, ana shigo da mutane daga waje don yin waɗannan kashe-kashen amma galibi, kamar a jaha ta, duk mutanen da muka kama, duk sun fito ne daga kudu maso gabas."

Kara karanta wannan

Ko a jikina asarar da na tafka, abu daya ne ya dame ni, Zuckerberg mai kamfanin Facebook

Gwamna Umahi ya ce gwamnonin yankin suna ci gaba da yin kira ga masu tayar da kayar baya da su kawo korafinsu gaba, tare da yin alkawarin samar da mafita.

“Ko menene matsalar ku, rashin aikin yi ne, ba ku da abin yi? Za mu bar kowane abu don tabbatar da cewa an ba ku tallafi. Abinda yake kawai shine lokacin da kuke cikin daji, bamu da damar zuwa gare ku. Dole ne ku fito daga daji ku yi aiki tare da mu don tallafa maku.
"Amma a lokacin da kuka ce a'a, cewa za ku tafi da sunan fafutika don haifar da laifi, za mu ware ku a matsayin masu laifi kuma a nan muke kuma da gaske muke kan haka."

Da yake magana game da umarnin zaman-gida, Umahi ya ce galibi mutanen da ke zaune a waje ne ke bayar da shi, kuma ya gurgunta ayyukan tattalin arziki a jihar.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Sanata na goyon bayan IPOB, ya ce akwai kungiyoyin aware a kudu sun fi 30

Gwamnan ya kuma koka da cewa mutanen kudu maso gabas suna yin biyayya ga umurnin zaman gidan ne kawai don tsoro ba wai don suna son yin biyayya ba.

Kashe-kashe: A bayyane ya ke, yaƙar jama'ar mu ake yi, Gwamnonin Kudu maso gabas

A gefe guda, Gwamnan jihar Ebonyi kuma shugaban kungiyar gwamnonin kudu maso gabas, Dave Umahi, ya ce sun gano cewa an kaddamar da yaki kan yankinsu a yayin da ya ke martani kan kashe-kashen da 'yan bindiga ke wa jama'arsu.

Kamar yadda Leadership ta ruwaito, Gwamna Umahi ya nuna damuwarsa da alhini kan kisan rayuka 12 da aka yi a yankin a makon da ya gabata kuma ya ce babu gaira balle dalili.

Gwamnan ya sanar da hakan ne yayin taron majalisar tsaro na jihar a ofishin sabon gwamnan Abakaliki. Ya zargi wasu Ndigbo da ke zama a kasashen ketare da shirya rigingimun tare da daukar nauyinsu.

Kara karanta wannan

Jama’a sun shiga halin fargaba yayin da ‘yan bindiga ke kafa sansani a birnin tarayya

Asali: Legit.ng

Online view pixel