Jerin yan arewa da Tinubu zai iya dauka a matsayin abokan takara idan ya shiga tseren shugaban kasa na 2023

Jerin yan arewa da Tinubu zai iya dauka a matsayin abokan takara idan ya shiga tseren shugaban kasa na 2023

  • Manyan yan siyasa a kasar na ci gaba da zawarcin kujerun shugabanci gabannin babban zaben 2023
  • Babban jigon jam’iyyar APC, Bola Tinubu na cikin wadanda ake ganin za su nemi takarar kujerar shugaban kasa
  • A wannan zauren, an lissafo wasu jerin yan siyasar arewa da ake ganin Tinubu zai zaba don yin takara tare

Asiwaju Bola Ahmed Tinubu yana da shahararrun abokai yan arewa da dama kuma waɗanda za a iya shigar da su cikin tawagarsa sannan a samu riba da su idan a ƙarshe ya bayyana sha'awar tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2023.

Kasancewar sa ɗan siyasa mara nuna kabilanci, babban jigon na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) yana da abokai da yawa daga dukkan yankunan Najeriya waɗanda ke da irin akidarsa ta siyasa.

Jerin yan arewa da Tinubu zai iya dauka a matsayin abokan takara idan ya shiga tseren shugaban kasa na 2023
Jerin yan arewa da Tinubu zai iya dauka a matsayin abokan takara idan ya shiga tseren shugaban kasa na 2023 Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

Sai dai kuma, tsohon gwamnan na Legas yana da damar zabar masu zurfin tunani ne kawai daga jam’iyyarsa ta siyasa, wato APC.

Read also

Atiku Abubakar ya yi magana kan yankin da ya kamata PDP ta kai takarar shugaban kasa a 2023

A halin da ake ciki, wasu rukuni na manyan ‘yan arewa ne za su iya zama abokan takarar Tinubu tunda zai fi so ya zaɓa daga yankin don nuna halayen mulkinsa.

Wasu, idan ba duka ba, daga cikin waɗannan 'yan arewan, har yanzu ba su riga sun bayyana burinsu na shiga babban zaɓen kasar mai zuwa ba. Su ne:

1. Babban Lauyan Tarayya (AGF) Abubakar Malami

2. Gwamna Nasir El-Rufai na Kaduna

3. Gwamna Simon Lalong na Filato

4. Gwamna Abdullahi Ganduje na Kano

5. Yakubu Dogara

6. Gwamna Babagana Zulum na Borno

7. Gwamna Aminu Bello Masari na Katsina

8. Gwamna Bello Matawalle na Zamfara

9. Sanata Ali Ndume

Dalilin da yasa na kira Tinubu 'Shugaban kasa' a kasar waje - Dan majalisa yayi bayani kan bidiyon da ya bazu

Read also

2023: Jigon APC da ya shiga gidan yari ya fito, yana maganar neman Shugaban kasa

A gefe guda, Wani dan majalisar wakilai, Abubakar Lado Suleja (APC, Niger) ya yi bayanin bidiyon da ya shahara, wanda a ciki ya kira Asiwaju Bola Tinubu, a matsayin ‘Mai girma Shugaban kasa’ a lokacin da suka ziyarce shi a Landan a makon da ya gabata.

Shugabannin kungiyoyin Arewa na APC, karkashin jagorancin mataimakin kakakin majalisar, Ahmed Wase, sun ziyarci Tinubu a Landan a ranar 1 ga watan Oktoba.

A cikin bidiyon, Suleja ya cewa Tinubu yayin da ya yi kokarin shiga motarsa: "Mai girma Shugaban kasa, sai anjima." Tinubu ya amsa da "Na gode."

Source: Legit.ng

Online view pixel