Kasurgumin dan ta'adda mai daukar bidiyo ga Boko Haram ya mika wuya ga sojoji

Kasurgumin dan ta'adda mai daukar bidiyo ga Boko Haram ya mika wuya ga sojoji

  • Kasurgumin dan ta'addan Boko Haram da ke daukar hotunan bidiyo ga 'yan ta'addan Boko Haram ya mika wuya
  • A halin yanzu rahoton tsaro ya ce mutumin yana hannun gwamnatin jiha don ci gaba da tatsar bayanai daga gare shi
  • 'Yan Boko Haram na ci gaba da mika wuya ga jami'an tsaro a baya-bayan nan biyo bayan mutuwar shugabansu

Borno - Wani mai daukar hoton bidiyo da ke aiki tare da kungiyar ta’addanci, Boko Haram, ya mika kansa ga jami’an gwamnati a jihar Borno da ke a Arewa maso gabashin Najeriya, in ji wata majiyar tsaro.

Mai daukar hoton bidiyon wanda har yanzu ba a bayyana sunansa ba, a halin yanzu yana tsare a wani gidan gwamnati tare da daruruwan sauran 'yan ta'adda da suka mika wuya, HumAngle ta ruwaito.

Read also

Yan sanda sun kame waɗanda ake zargi da kisan babban malamin Addini a jihar Kano

Kasurgumin dan ta'adda mai daukar bidiyo ga Boko Haram ya mika wuya ga sojoji
Taswirar jihar Borno | Hoto: thenationonlineng.net
Source: Facebook

Babban jami'in gwamnatin jihar Borno ya ce:

"Yanzu muna da daya daga cikin manyan masu daukar hoton bidiyo da suka saba daukar bidiyon Boko Haram a hannunmu."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Ya mika kansa ga sojojinmu kuma ya fito da dukkan kayansa da suka hada da kwamfutocin tafi-da-gidanka da kyamarori masu inganci. Yana nan tare da mu kuma yana ba mu goyon baya sosai tare da bayanai kan yadda za a sa wasu su fito su kuma mika wuya.”

Mambobin kungiyar JAS na Boko Haram suna mika kansu a kullum.

Jami'in ya kara da cewa:

"Kamar yadda yake a yanzu, muna da mayaka sama da 790 wadanda a halin yanzu suna hannunmu bayan sun mika kansu da son ransu."

A makon da ya gabata ne rundunar sojin Najeriya ta ce sama da mayakan Boko Haram 8000 da iyalansu sun mika wuya ga sojoji a Borno da wasu jihohin arewa maso gabas.

Read also

'Yan fashi sun afka wa coci domin sace kudi, sun daba wa mai gadi wuka a Abuja

Sai dai majiyar ta yi karin haske da cewa "ba duk wadanda suka mika wuya ba ne ainihin mayakan Boko Haram."

A cewar majiyar:

"Lokacin da 'yan Boko Haram suka mika wuya sai suka fito tare da wasu mutane da yawa kamar matansu da yaransu, kamar manoma da aka tilasta su ci gaba da zama a yankunansu don yin aikin noma da sauransu."

Majiyar ta ce ana kuma ci gaba da tantance na gaskiya da na karya a cikin tubabbun 'yan ta'addan.

Majiyar ta kara da cewa hatta mayakan na gaskiya sun taimaka wa jami'an gwamnati a wurin da ake tsare da su don gano 'yan Boko Haram din da ba sa yaki ta hanyar tabbatar da ikirarin su na rashin aikata laifi.

Kasurgumin shugaban 'yan bindiga ya tona asirin 'yan uwansa, ya nemi gafara

Goma Samaila, shugaban gungun masu garkuwa da mutane a yankin Rigachukum ta jihar Kaduna, ya bayyana sunayen mambobin kungiyar sa, Daily Trust ta ruwaito.

Read also

Shekarau ya ba Gwamnonin jihohin Kudu shawara, yace su daina barazana kan batun 2023

Mutumin mai shekaru 47, wanda rahotanni ke cewa ya dade yana tafka ta'annuti, ya yi magana kan wasu ayyukansa da adadin kudin da ya karba a matsayin kudin fansa.

A wani faifan bidiyo, an ga Samaila yana rokon gafara yayin da daya daga cikin jami'an tsaron da ya kama shi ke tambayarsa.

A cewarsa:

“Ina rokon jinkai da gafara; Ba zan sake aikata irin wannan laifin ba."

Dangane da wasu ayyukan da ya yi, ya ce:

“Mutum na farko da muka yi garkuwa da shi shine Abdul; sun biya kudin fansa N200,000; akan Alhaji Umaru, mun karbi N500,000, Wani kuma Alhaji Birau; sun biya jimillar naira miliyan uku sannan dayan kuma shine Alhaji Ibrahim wanda ya biya N700,000.”

Mahaifin kakakin majalisa da malamin jami'a sun mutu a hannun 'yan bindiga

A wani labarin, Alhaji Muazu Abubakar, mahaifin kakakin majalisar jihar Zamfara, Nasiru Muazu Magarya, ya rasu sakamakon bugun zuciya yayin da yake tsare a mafakar 'yan bindiga.

Read also

Labarin gimbiyar da ta bar masarautarsu ta auri talaka ya dauki hankalin jama'a

Babban dan uwan marigayin, Malam Dahiru Saraki Magarya ne ya bayyana hakan a wata hira da aka yi da shi a ranar Asabar, kamar yadda jaridar Blueprint ta ruwaito.

An yi garkuwa da marigayin ne makonni takwas da suka gabata tare da matarsa, jariri dan makonni uku, Malam Magarya da wasu mutum biyu.

Source: Legit.ng

Online view pixel