Shekarau ya ba Gwamnonin jihohin Kudu shawara, yace su daina barazana kan batun 2023

Shekarau ya ba Gwamnonin jihohin Kudu shawara, yace su daina barazana kan batun 2023

Malam Ibrahim Shekarau ya yi magana game da siyasar 2023 da jam’iyyar APC

Sanatan na jihar Kano ta tsakiya ya soki salon gwamnonin kudancin Najeriya

Shekarau yayi kira ga APC ta kai takarar 2023 zuwa Kudu domin a tafi da kowa

Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau yace gwamnonin kudancin Najeriya 17 su daina yi masu barazana game da zaben 2023.

Ibrahim Shekarau wanda yanzu Sanata ne mai wakiltar Kano ta tsakiya a majalisar dattawa ya bayyana haka da aka yi hira da shi a gidan Channels Television.

Shekarau ya sake jaddada ra’ayinsa na cewa ya kamata shugaban kasar da za ayi a 2023 ya fito daga kudancin Najeriya domin kowane yanki ya ji ana yi da shi.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC za ta yaki satar kudin fanshon ma’aikata, wasu mutane sun wawuri N150bn

Jaridar Punch ta rahoto Sanatan yana kira ga jam’iyyar APC ta kai takarar shugaban kasa zuwa kudancin Najeriya, sannan a zakulo ‘dan takarar da ya cancanta.

Amma duk da haka tsohon Ministan ilmin ya soki taron dangin da gwamnonin jihohin kudu suke yi.

Ibrahim Shekarau yake cewa ‘yan jarida lamarin 2023 ya zama abin takaici inda har ta kai maganar karba-karba ya na nema ya zama wani taron dangin bangare.

Shekarau
Ibrahim Shekarau da Jonathan Hoto: www.premiumtimesng.com

Da yake bayani a ranar Litinin, 4 ga watan Oktoba, 2021, Shekarau yayi kira ga gwamnonin su tattauna a jam’iyyunsu, su yanke shawara kafin su fito waje.

“Shawarar da nake ba jam’iyya ta, APC, ita ce, Buhari ya fito ne daga Arewa, bayan ya yi shekaru takwas, sai a nemo magajinsa daga yankin kudancin Najeriya.”

Kara karanta wannan

Hadimin Jonathan ya bayyana kudirin neman takarar Shugaban kasa, ya shimfida alkawura

“Ba wai domin ba mu da wadanda suka dace a yankin Arewacin kasar ba, kuma hakan ba ya nufin za ayi watsi da cancanta, da nagartar ‘dan takara da sauransu.”
“Ban yarda da gwamnonin Kudu da suke gayya suna cewa dole a ba su mulki ba. Wannan sha’ain jam’iyya ne. Ba sai an kai ga yin barazana ba, siyasar gida ce.” - Shekarau

Bicike ya fallasa wasu 'yan siyasa

Wasu ‘Yan siyasa da ake ji da su za su raina kansu bayan fitowar rahoton Pandora Papers. Daga cikinsu har da babban jigon jam'iyyar PDP na kasa, Peter Obi.

Binciken da aka gudanar ya tona wa ‘Yan siyasa sama da 300 a kasashen Duniya. Daga cikinsu akwai tsofaffin gwamnoni da wasu 'yan majalisa daga Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel