Labarin gimbiyar da ta bar masarautarsu ta auri talaka ya dauki hankalin jama'a
- Wata gimbiya ta yi watsi da dukkan jin dadin gidan sarauta ta auri wani talaka gama-gari
- Wannan na zuwa ne bayan haduwarsu a shekarar 2012 a makaranta, lamarin mai ban sha'awa
- Jama'a sun yi martani kan masoyan, inda Legit.ng ta tattaro muku maganar jama'a kan batun
Aljazeera ta ruwaito cewa za a daura auren gimbiya Mako ta kasar Japan da wani talaka mai suna Kei Komuro a watan Oktoba na 2021.
A baya kada, an lura cewa ma'auratan sun yi ta yawo a kafafen yanar gizo kwanaki da suka gabata bayan dangantakar su ta zama sananniya ga jama'a.
Ta bar sarautarta saboda talaka
Domin ta auri mutumin da kowa yasan gama-gari ne kuma talaka, gimbiyar za ta ba da matsayin sarauta da gadon ta da ya kai biliyoyin kudade.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A wani faifan bidiyo da Aljazeera ta yada, ma'auratan sun hadu da juna ne a shekarar 2012. An ce Komuro wanda lauya ne da ake fafatawa dashi a kasar Amurka.
Yadda suka shirya aurensu
An soke shirin ma’auratan na yin aure a shekarar 2018 bayan rahotanni da aka samu sun ce dangin angon na fuskantar matsalar kudi.
Ko da yake a kasar Japan ana tube mace daga sarautarta lokacin da ta bukaci auren talaka, hakan bai shafi maza ba. Rashin samun isassun maza a cikin iyali yana haifar da rikicin maye gurbinsu.
Martanin jama'a
Legit.ng ta tattaro martani kan yadda jama'a suka ji game da wannan labarin soyayya a kafafen sada zumunta.
inakablues ya ce:
"Yayi mata kyau ... ki fita yayin da zaki iya!"
surmeydee ya ce:
"Girmama ... kamar almara ... soyayya tayi nasara."
tayatanzy ya ce:
"Kenan muna da Gimbiya 2 a Amurka yanzu."
marilyne_13 ya ce:
"Wannan ya wartsakar da zuciyata, ya ruda ni kuma ya girgiza ni gaba daya. Dokin soyayya ne ya dauke su .. wannan abin dariya ne."
daidaiedevereaux ya ce:
"Barka da zuwa kasarmu, Gimbiya. Inda mata ke yin duk abin da muke so (kawai ku guji Texas)."
Asali: Legit.ng