Yan sanda sun kame waɗanda ake zargi da kisan babban malamin Addini a jihar Kano

Yan sanda sun kame waɗanda ake zargi da kisan babban malamin Addini a jihar Kano

  • Rundunar yan sanda reshen jihar Kano, ta bayyana cewa ta damke mutum 7 da ake zargin suna da hannu a kisan wani malami a Kano
  • Kakakin yan sandan jihar, Abdullahi Kiyawa, yace mutanen sun ce, suna zargin shugaban CAN da ɓoye wani mai laifi
  • Rahoto ya nuna cewa Fasto Yohanna, ya jefa kanshi a cikin lamarin wani mutumi da mutane ke zargi da hallaka matar yayansa

Kano - Rundunar yan sanda ta tabbatar da kame mutun 7 dake da hannu a kisan shugaban ƙungiyar kiristoci (CAN) na ƙaramar hukumar Sumaila, jihar Kano, Shuaibu Yohana, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Mista Yohanna, babban malamin addinin kirista, ya rasa rayuwarsa ne a hannun wasu mutane kwanaki kaɗan da suka gabata.

Read also

Da duminsa: Masu garkuwa da mutane sun sace dalibar BUK a Kano

Shugabannin ƙungiyar kiristoci na jihar Kano sun yi kira ga hukumomi da su tabbatar da adalci a kan ran ɗan uwansu.

Yan sanda
Yan sanda sun kame waɗanda ake zargi da kisan babban malamin Addini a jihar Kano Hoto: dailypost.com
Source: UGC

Meyafaru da marigayi Fasto Yohanna?

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya fara ne ranar 22 ga watan Satumba, lokacin da wani Sabo Idris, ya kashe matar yayansa, bayan samun sabani.

Sai dai Fasto Yohanna, ya shiga cikin lamarin, inda mutane suka fara zarginsa da ɓoye Idris, wanda ya canza addini zuwa addinin kirista.

Bisa haka ne fusatattun mutanen yankin suka hallaka faston, kuma suka kone cocinsa, gida da kuma makarantar da yake jagoranta.

Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?

Da yake fira da BBC Hausa ranar Litinin da yamma, kakakin yan sanda na jihar Kano, Abdullahi Kiyawa, yace jami'ai sun damke mutum 6 a wurin da aka aikata kisan.

Read also

Jama’a sun shiga halin fargaba yayin da ‘yan bindiga ke kafa sansani a birnin tarayya

Kiyawa yace:

"A binciken yan sanda, waɗanda ake zargin sun bayyana cewa sun zargi faston da ɓoye wani mutumi da ya kashe matar yayansa."
"Daga baya wani mutum ɗaya ya kawo kansa, a halin yanzun mun kama mutum 7 dake da hannu a kisan faston."
"Wannan babban lamari ne da ba zai yuwu a kammala shi lokaci ɗaya ba. Muna bukatar hujja kuma yanzun muna kan hanyar bincike."

A wani labarin na daban kuma Kamfanin sada zumunta Twitter ya yi martani kan kalaman shugaba Buhari na ranar samu yancin kai

Dandalin sada zumunta Twitter ya nuna jin daɗinsa bisa kalaman shugaba Buhari na ɗage hanin da aka masa idan ya cika sharuɗɗa.

A cikin jawabinsa na ranar yancin kai, Buhari yace gwamnati a shirye take ta ɗage hanin amfani da twitter da zaran an cimma matsaya.

Source: Legit.ng

Online view pixel