'Yan fashi sun afka wa coci domin sace kudi, sun daba wa mai gadi wuka a Abuja

'Yan fashi sun afka wa coci domin sace kudi, sun daba wa mai gadi wuka a Abuja

  • Tsagerun 'yan fashi sun afkawa coci domin su kwashi kudi, amma basu samu komai a ciki ba
  • Rahoto ya bayyana cewa, an daba wa wani mai gadi wuka a bakin cocin yayin da yayi kokarin dakatar dasu
  • Rundunar 'yan sanda basu samu rahoto kan lamarin ba, amma cocin ya ce ya kai rahoto ga 'yan sandan

Abuja - Tsoro ya mamaye mazauna unguwar District Center Estate, Phase 4, Kubwa, a karamar hukumar Bwari da ke Babban Birnin Tarayya, Abuja, bayan farmakin da wasu da ake zargin 'yan fashi sun kai Cibiyar Injila ta Duniya ta Dunamis.

An bayyana cewa tsagerun sun soki wani mai gadi, wanda aka bayyana sunansa da John a ciki sannan suka yage hanjinsa waje, Punch ta tattaro.

'Yan fashin, wadanda yawansu ya kai 10, an ce sun zo cocin ne daga kauyuka da unguwannin makwabta da ke yankin.

Read also

Ba ma son Biyafara, kawai muna so ayi mana adalci daidai da kowa ne - Gwamna Umahi

'Yan fashi sun afka wa coci domin sace kudi, sun daba wa mai gadi wuka a Abuja
Taswirar birnin tarayya Abuja | Hoto: nigeriazipcodes.com
Source: UGC

Wata majiya ta ce sun nemi kudi kuma sun yi bincike a harabar cocin, ta kara da cewa sun fusata lokacin da ba su samu komai ba.

A kalaman majiyar:

“Lamarin ya faru da misalin karfe uku na safiyar Litinin. 'Yan fashin sun zo kuma John ya yi kokarin gwagwarmaya da su. A lokacin da suke rikicin, sun rinjaye shi kuma sun soke shi a ciki.
“An garzaya da shi babban asibitin Kubwa amma saboda likitoci na yajin aiki, babu abin da za a iya yi. Daga nan aka mayar da shi wani asibiti mai zaman kansa a Abuja.”

Shugaban rukunin gidajen gundumar, Ifeanyi Uwaje, ya tabbatar da faruwar lamarin.

A cewarsa:

“Abin da ya faru abin takaici ne matuka; mun kai wanda abin ya rutsa da shi asibiti kuma mun kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda.”

Read also

Ko a jikina asarar da na tafka, abu daya ne ya dame ni, Zuckerberg mai kamfanin Facebook

Wani Fasto na cocin, Joseph Ogaba, ya ce babu abin da aka sace daga cocin.

A kalamansa, cewa yayi:

“Ba a saci komai daga cocin ba kuma ba za mu iya tambayar mutumin (mai gadi) da ke kan gadon asibiti ba. Har sai ya samu sauki kuma mun ji daga gare shi, duk abin da kuka ji zai iya zama zato. Za mu fi son ku jira ku ji daga coci kafin bugawa.”

Jami’ar hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda na babban birnin tarayya, DSP Josephine Adeh, ta ce ba a yi mata bayanin abin da ya faru ba.

Duk da haka, ta yi alkawarin za ta ba da bayani da zaran rahoton ya zo mata.

Lokacin da aka tuntube ta daga baya, ta ce har yanzu ba a yi mata karin bayani ba daga ofishin ‘yan sanda na yankin Kubwa.

Jami'an NSCDC sun cafke abokin harkallar 'yan bindiga dauke da karamar bindiga

Read also

Babbar Magana: Sanata na goyon bayan IPOB, ya ce akwai kungiyoyin aware a kudu sun fi 30

Hukumar tsaro ta NSCDC, ta cafke wani da ake zargi mai hada gwiwa ne da kuma ba 'yan bindiga bayanai wajen garkuwa da mutane da ke barna a cikin garin Enugu da kewayenta, Daily Nigerian ta ruwaito.

Hukumar ta kwato N2,100, katunan ATM guda uku, wayoyin hannu guda biyu, kunshin wani abu da ake zargi tabar wiwi ne da kuma karamar bindiga da aka boye a karkashin wasu abubuwan a cikin karamar jaka da sauransu.

Jami'in hulda da jama'a na hukumar NSCDC, reshen jihar Enugu, Danny Manuel, ya fada a cikin wata sanarwa ranar Lahadi a Enugu cewa an kama wanda ake zargin ne a ranar 30 ga Satumba.

Mista Manuel, ya ce jami'ansu sun kama shi ne yayin aikin sintiri a yankin WTC Estate na Enugu da misalin karfe 2 na rana bayan daliban da suka dawo daga makaranta sun hango shi yana rike da bindiga wajen yin fashi ga wani mutum a yankin.

Read also

Jama’a sun shiga halin fargaba yayin da ‘yan bindiga ke kafa sansani a birnin tarayya

A cewarsa, wanda ake zargin shine Oguchi Oguamanam, namiji mai shekaru 24, wanda ke zaune a 7 Monarch Avenue daura da Timber Junction kusa da garin Ugwu-Aji a cikin garin Enugu.

Rahoto: Halin da ake ciki na harin 'yan bindiga duk da katse hanyoyin sadarwa a Zamfara

A wani labarin, alamu sun bayyana cewa har yanzu ana ci gaba da samun kashe-kashe da garkuwa da mutane a jihar Zamfara duk da katse hanyoyin sadarwa a jihar.

Yayin da katsewar da kokarin sojoji ya rage barnar 'yan bindiga tare da kashe su, wasu mazauna jihar sun shaida wa BBC Hausa cewa an ci gaba da kai hare-hare da sace-sacen a jihar.

Don haka, duk da rokon da suke yi wa gwamnatin jihar na tsagaita wuta, kamar yadda Gwamna Bello Matawalle ya bayyana a ranar 10 ga Satumba, 'yan bindigan sun ci gaba da kai hari kan mazauna jihar.

Read also

Bishiya mai shekaru 100 ta fadi kan mutane, ta hallaka jariri da mahaifiyarsa

Source: Legit.ng

Online view pixel